Neman man fetur a Arewa: An samu rabuwar kai a hukumar NNPC

0 5

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Masu fada aji a harkan man fetur ba su gushe ba su na karo da junan su game da binciko man fetur a Arewa,
musamman da a yanzun har an kashe miliyan 3 na dalar Amurka ba tare da an samu nasara ba.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewan
masu goyon bayan cigaba da binciken, basu damu da barnar kudin da a ke yi ba sakamakon nasarar hakon mai da a ka samu a makotan kasashe irin su Nijar da Chadi.

Su kuwa masana ilimin hako ma’adanai su na tunanin aikin banza a ke yi.

Arewaclass ta tattaro bayanan masana a inda su ke cewa, kowace yanki na Najeriya da albarkatun da Allah ya yi mata, ba zai yiwu man fetur da albarkatun da ke Arewa su zauna tare a wuri daya ba.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

A tattaunawar da Jaridar Guardian ta yi da masana, sun ce shuwagabannin Arewa, cikin su har da Shugaban Kasa Buhari, sun matsa kan binciken wanda hakan na illata tattalin arzikin kasan.

Kusan shekaru 40 kenan da fara binciko man fetur a Arewa, a ra’ayin wadansu ana hakan ne kawai don azurta kalilan din mutane.

Shi kuwa Shugaban NNPC, Maikanti
Baru, ya ce ba za su gushe su na
wannan bincike ba matukar umurni ne daga Buhari.

Ya kuma ce a bisa binciken da su ka yi, nan ba da jimawa ba za’a iya samo man fetur mai yawa a
Anambra, Bida, Benue, Chad, Gongola, da Sokoto.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.