[Neman Duniya] Wani Mutum Ya yanka Yarsa

32

Advertisement

John Depuun ya yanka jaririyar ‘yar shi don yin tsafi a wani kauye mai suna Tse-Agberagba, karamar hukumar Konshisha dake jihar Binuwai, ciyaman din karamar hukumar ne ya tabbatar da afkuwar lamarin yau Alhamis.

Tuni da aka sanar da rundunar ‘yan sandan jihar wannan danyen aikin da Mista Depuun ya aikata, jami’an ‘yan sanda basu yi wata-wata ba wajen cafke shi.

Zuwa yanzu rundunar ‘yan sanda ta ce tana kan gudanar da bincike akan mutumin, kuma da zarar ta kammala binciken nata za ta gurfanar da mutumin a gaban kotu don fuskantar hukuncin da ya dace.

Allah ya kare mu Yasa mufi Karfin Zukatan mu. Ameen

©leadershipayau

Leave a Reply