Nasarorin da shugaba Buhari yasamu

0

Babban mai taimaka wa shugaban kasa MUHAMMADU BUHARI akan harkar watsa labarai Garba Shehu yace a wannan shekaran
gwamnati ta rage asaran da take yi na biyan albashi a kowani wata ga ma’aikatan boge.

Garba Shehu yayi bayanin hakanne a wata ganawa da yayi da ‘yan jarida a Abuja.

Yace gwamnati na biyan kudin da ya kai biliyan 200 a kowani wata amma bayan ta gama binciken sahihan ma’aikatan gwamnatin tarayyan sai ta gano cewa sama da ma’aikata
50,000 na boge ne wanda wadansu ne ke amfani da sunayensu domin wawushe kudaden gwamnati sannan gwamnati ta kama
wadansu manyan ma’aikatan ta guda 11 da suke da hannu akan hakan kuma ta mika su ga hukumar EFCC domin a bincikesu.

Garba Shehu ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta zake da sai ta kawar da duk wani irin cin hanci da rashawa a kasar domin kuwa
zata cigaba da tantance ma’aikatan ta domin tabbatar da ta gano masu shirya irin wannan aiki da karerayi.

Da yake magana akan ‘yan matan Chibok wanda aka ceto su daga hannun Boko Haram Ya ce gwamnati ta dauki nauyin kula da ‘yan matan amma a yanzu haka mutane da kungiyoyi dayawa da ke kasar nan da wadansu daga kasashen waje sun nuna suna
son su dauki nauyin ‘yan matan musammman akan abinda ya shafi karatunsu kamar wani
hanshakin mai kudi mai suna Robert Smith kuma mazaunin kasar Amurka da ya dauki
alkawarin biyan kudin makarantar ‘yan matan guda 21 da kuma sauran da sojoji za su ceto har zuwa jami’a, da kuma gidauniyar Murtala Muhammed da ta yi irin wannan tayin.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Duk da haka wasu iyayen ‘yan matan sun mkoka da yadda ‘yan sandan farar hula ba su bar ‘yan matan sun je gidajen iyayen su ba
domin su yi bukin krismati duk da cewa suna cikin garin Chibok.
Shugaban ‘yan sandan farar hulan wato SSS yace dalilin yin haka shine domin sun sami ‘yan matsaloli ne kan tsaron yan matan.

NOMA

Garba Shehu yayi bayanin cewa ganin yadda shugaban kasa ya ke da muradin ganin cewa aikin gona ya dawo da martabarsa a kasa
Najeriya a wannan shekaran gwamnati ta taimakawa manoma sannan a na sa ran za’a samu kayan gona wadatacce domin ci da
siyarwa a kasa Najeriya da kasashen waje kuma hakan ya farantawa manoma rai domin a
yanzu haka sababbin tsaruka da shirye shirye ne gwamnati ta fara domin samun ire-iren wadannan nasarori a damiman badi.

Wani abin da ya farantawa manoma ciki shineyadda gwamnati ta hana shigowa da kayan abinci musamman shinkafa kuma ta shawarci manyan kamfanoni kamar su Nestle, Unilever da sauran su da su duba su gani ko akwai
abin da za su iya amfani da shi wanda kasar ke nomawa a maimakon su siyo a kasashen wake.