Mutum 500,000 na na cikin tasku a Barno

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ƙungiyar agajin likitoci ta Medicins Sans Frontieres ta ce aƙalla mutum dubu dari biyar da suka maƙale a wasu sassan jihar Borno da rikicin Boko Haram ya shafa suna buƙatar agajin gaggawa. MSF ta ce waɗannan mutane suna buƙatar agajin, abinci da magunguna, da ruwan sha da kuma matsugunni. Kungiyar agajin ta MSF ta wallafa bayanai a shafinta na intarnet dangane da irin taskun da mutane suke fuskanta kafin su kai ga samun asibiti, da abinci da ruwan sha. MSF ta wallafa bayanan wasu mata biyu domin nuna misalin irin yadda wannan matsalar ke shafar jama’a. Tsawon shekarun da aka kwashe ana rikicin Boko Haram ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali a jihar Borno, inda aka kwashe shekaru a wasu wuraren jama’a ba sa iya noma. A wasu wuraren MSF ta ce, kasuwanni basa ci, kuma hanyoyin da ake bi domin zuwa fatauci sun kasance wasu a rufe, wasu kuma binsu yana cike da hatsari. Kungiyar agajin likitocin ta MSF tace, yanzu haka akwai mutane fiye da miliyan daya da rabi a Maiduguri dake zaman gudun hijira, yawancinsu kuma ‘yan’uwansu ne suka basu matsugunni. Kuma akwai wasu mutanen da dama da suke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.