Mutum 13 sun mutu a maiduguri

0

Rahotanni daga birnin Maiduguri arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani harin kunar-bakin-wake a tashar Muna ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 13, ko da yake, hukumomi na tabbatar da mutuwar mutum takwas.

Wasu ‘yan harin kunar bakin wake guda uku ne suka kai harin na Muna Garage da ke wajen birnin Maiduguri a jihar Borno yankin arewa maso
gabashin Najeriya.

‘Yan kunar bakin waken wadanda hukumomi suka ce mata ne, sun kai harin ne da maraicen ranar Lahadi, inda guda ta tayar da bam din ta,
sauran biyun kuma, daya ta fadi amma bai dai bam din bai fashe ba.

Sai dayar kuma wadda ta sulale ta shiga gari lamarin da ya sa jami’an tsaro suka shiga farautarta ko da yake babu tabbacin ko akwai bam a jikinta ko kuma ta cire.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar SEMA, Injiniya Satomi Ahmad, ya ce ya zuwa daren ranar Lahadi sun kwashi gawawwakin
mutum takwas ban da wadda ta kai harin, yayin da 14 kuma suka samu rauni.

Injiniya Satomi, ya ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu sakamakon hari ya karu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Ya kuma ce a cikin shekarar nan kadai, an kai harin kunar bakin wake Garejin Muna sau 13, sai dai babu wanda aka fi samun mutuwa sai
wannan.

Harin na maraicen Lahadi, ya zo ne bayan an samu lafawar hare-haren ‘yan ta-da-kayar-baya a yankin.

A karshen watan Yuli ne, Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya umarci manyan hafsoshin tsaron Najeriya su koma birnin Maiduguri da zama.

Manyan hafsoshin tsaron sun tare a can din ne bayan wani mummunan hari da kungiyar Boko Haram ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar fiye
da mutum 40.

Source: bbchausa.com