Musulmi mata na cikin kangi a Birtaniya

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wani rahoto da majalisar dokokin Birtaniya ta fitar ya ce
Musulmi mata na samun koma-baya a fannin tattalin
arzikin kasar.
Rahoton ya gano cewa musulmi mata suna fuskantar
yiwuwar rashin samun aiki sau uku idan aka kwatanta
da sauran mata.
Ya bayyana wani mawuyacin hali da matan suka fi
fama da shi – wato kasancewarsu mata da
kasancewarsu daga tsirarun al’umma da kuma
kasancewarsu Musulmi.
‘Yan majalisar sun ce ya kamata ministoci su bullo da
wasu tsare-tsare masu inganci da za su kawo karshen
wannan matsala kafin karshen shekarar nan.
Wani mai magana da yawun gwamnatin kasar ya ce
yanzu musulmi mata kashi 45 cikin 100 na yin aiki
idan aka kwatanta da shekara biyar da suka wuce, ko
da yake ya amince cewa akwai bukatar zage dantse
domin taimaka musu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.