Musayar wuta tsakanin bangarori 2 na APC

0
‘Yan kasuwa, masu shaguna da masu wucewa sunyi gudun rayukan su a titin Onyeamekun da ke garin Akure a jahar Ogun a jiya Alhamis a yayin da rikici ya barke tsakanin bangarori biyu na jam’iyyar APC na jahar, al’amarin har ya kai ga musayar wuta tsakaninsu a harabar sakateriyar jam’iyyar. Rikicin ya auku ne tsakanin magoya bayan shugaban jam’iyyar reshen jahar Ogun Isaac Kekemeke da sauran ‘yan jam’iyyar, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto. A ranar Talatar da ta gabata ne wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar suka rufe sakateriyar bayan da suka sanar da cewa sun sauke shugaban jam’iyyar. A ranar Laraba, Sun kara bude sakateriyar sannan suka kori dukkanin ma’aikatan sakateriyar. Sai dai al’amura sun yi tsami a jiya Alhamis a yayin da magoya bayan shugaban suka ziyarci sakateriyar da nufin tada tarzoma. Sai da mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jahar Edward Ajogun ya ziyarci harabar sakateriyar tukunna rikicin ya lafa.