Muna Da Matukar Anfani a Alumma Amma kuma Suna Kushe mu

0 4

Advertisement

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan
Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fis ani da Hadizan Saima

ta ce masu yin fina-finan na Hausa sun zama abin nan da Hausawa
ke cewa dankali sha kushe.
“Allah yana kallon abin da muke yi; idan
muna yi don mu bata ko mu gyara mu
fadakar, Allah ya sani.

“A cikin fina-finan da muke yi ana yin karatunA  l-Qur’ani, ana jan baki a fassara, ana ce wa’ Allah ya ce, Annabi ya ce’. Shi ma dukw annan koya rashin tarbiyya ne?”,
inji Hadiza, lokacin da take amsa tambayar da BBC ta yi mata kan zargin bata tarbiya da akey  i wa ‘yan fim.

Ta kara da cewa: “Ka san mu dankali ne sha
kushe, ana sonmu ana kushe mu. Amma hakaz a mu yi ta tafiya tun da haka Allah yayo mu.

“Haka za a yi ta hakuri da mu, mu ma muna
hakuri da masu kushe mu kuma a hankali za

su fahimce mu.

Na san wasu ma sun fahimta
yanzu.”

Jarumar, wacce akasari ta fi fitowa a
matsayin uwa, ta kara da cewa ta soma
sha’awar fina-finai ne tun lokacin da take daa  ure.

A cewarta, “Karance-karancen littafai da
kallon fina-finan tarihi ne suka sa na soma
sha’awar shiga fim.

“Na kalli fim din ‘Ki Yarda Da Ni’ a lokacin
ina gidan mijina, kuma da aurena ya zo
karshe sai na ji sha’awar shiga fim. Na soma
fim ne sama da shekara 16 da suka wuce
kuma na fito a fim fiye da 300.”

“Wani darakta ne marigayi Tijjani Ibrahim ya tambaye ni irin rawar da na fi so na taka a fim, ni kuma na ce masa na fi son fitowa a
matsayin uwa.

“Shi ya sa tun daga wancan lokaci nake
fitowa a matsayin uwa, tun ma ina da
kuriciya ake yi min kwalliya irin ta uwa domin nataka irin wannan rawar.”

©bbchausa

Leave a Reply