Mukashe PDP mu mika gawar ga sherrif- feni kayode

0 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohon ministan hada hadar jiragen sama a Nijeriya kuma dan jam’iyya mai adawa ta PDP ya kaiwa Shugaban daya bangaren jam’iyyar, Ali Modu Sheriff farmaki a jiya Laraba a shafunansa na kafofin sada zumunta na Twitter da Facebook. Fani dai ya yi watsi da shawarar daya daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar kuma tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Doyin Okupe na cewa bangaren Ahmed Makarfi ta shiga yarjejeniya da bangaren Modu Sheriff. Tsohon ministan wand ya kira Sheriff mafi girman kuskuren da jam’iyyar PDP ta taba tabkawa, ya bayyana cewa hanyar da jam’iyyar ya kama ta bi wajen warware matsalar da ta ke fuskanta shine ta ci gaba da yaki da Sheriff ta fagen shari’a ko kuma ta kashe PDP, ta barwar sheriff gawar tsohuwar, ta kafa sabuwar jam’iyya. Ya kara da cewa idan jam’iyyar ta yi haka, mutane kadan ne zasu kasance tare da Sheriff domin kuwa gawa ta kan yi wari, kuma saboda dama shine cutar da ke damun jam’iyyar. Fani da shi da sauran ‘yan jam’iyyar ta sa na zargin cewa jam’iyyar APC na amfani da Sheriff ne wajen yunkurin hargitsaPDP. Jam’iyyar wacce ta kara soke gangamin taron ta, ta kara wa’adin rikon shugabancin jam’iyyar da ta baiwa Ahmed Makarfi da shekara daya, domin samun lokacin da zata warware matsalolin shari’ar da ta ke fuskanta kafin ta yi wani taron.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.