Mukan zuwa daji don tsinko tafasa muci da yayan mu

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Alƙaluma na baya-bayan nan da ƙungiyar likitoci ta Medecin sans frontiere ta fitar, sun nuna cewa mutanen da ke matuƙar buƙatar agajin gaggawa a Najeriya sun haura 500,000. Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar da ke arewa-maso-gabashin Najeriya da BBC ta zanta da su sun ce suna yin bara kuma suna shiga daji domin yin tafasa. An jima ana zargin cewa wasu batagari na sauya akalar abincin da ya kamata a kai wa ‘yan gudun hijirar. Gwamnati ta ce ta fara bincike a kan lamarin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.