MTN Zata biya Dalar Amuruka miliyan 52.6

0

Jaridar nan ta Daily Nigerian mai wallafa labarai a shafunan gizo ta bayyana mana wannan a farkon wannan makon. Jaridar kasar tace kamfanin na MTN ya amince ya biya Najeriya wadannan makudan kudi a dalilin laifin da su kayi.

Bankin CBN, wanda shi ne babban bankin Najeriya, ya nemi kamfanin sadarwan na MTN da su biya gwamnatin Najeriya Dala miliyan 52.6 saboda badakalar takardun wasu satifiket na kamfanin da aka yi ba tare da cika sharuda ba.

Bayan doguwar zantawa da kai kawo, an ci ma yarjejeniya tsakanin babban bankin na Najeriya da kuma kamfanin, inda MTN ya amince ya biya wadannan makudan kudi wanda sun haura Biliyan 15 a kudin Najeriya na gida watau Naira.

KARANTA WADANNAN;
1 of 93

Kamfanin na MTN ya bayyana wannan ne a Ranar Litinin dinnan inda ya fitar da wani jawabi mai nuna cewa sun cin ma yarjejeniya tsakanin su da gwamnatin Najeriya. An yi wannan zama ne dai a Garin Legas da ke kudancin Najeriya.

A jawanin da aka fitar, MTN ya shirya biyan wannan makudan kudi domin ayi sulhu da Najeriya na sabawa wasu dokoki da aka yi wajen karbar takardun shaida da ke bada dama a shigo da kaya cikin kasar nan da nufin kasuwanci.

#legithausa