Matar da tayi yun kurin kashe Mijinta Ta sacce Lefen Amarya

1 15

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

 

Matar Da Ta Yi Yunkurin Kashe Mijinta Ta Sace Lefen Amarya

Matar nan mai suna Rabi’a Usman Muhammad KK, wacce a ke yiwa lakabi da Mami, ta sadada gidan tsohon mijinta, Nasir Sa’ad, a Kano ta sace kayan lefen da ya tanada ga amaryar da zai auro.

credited by arewablog.

Rabi’a ta aikata hakan ne tare da hadin gwiwar wata yayarta da ’yar babbar yayarta da kuma wasu mutane wadanda dukkansu a nan gaba majiyar jami’an tsaro ta ce za a bayyana sunayensu a caji ofis din ’yan sandan da a ka riga a ka shigar da korafi ko kuma a kotun da za a gudanar da shari’a kan zargin sace kayan.

KARANTA WADANNAN;
1 of 96

Lauyan tsohon mijin, Barista Nazir Adamu, wanda ya tabbatar wa da wakilinmu tuni an shigar da korafin a cafi ofis da ke GRA na Dorayi Babba Cikin Gari, ya kara da cewa, a na zargin Rabi’a tare da na hannun damanta da yin gaban kansu ne a ranar 27 ga Maris, 2018 ne, inda su ka durfafi gidan tsohon mijin da sunan za ta kwashi kayanta, duk da cewa ta san ba ya gari kasancewarsa ma’aikaci a babban birnin tarayya Abuja, amma su ka yiwa muhimman kayansa wawaso.

A cikin kayayyakin da a ke zargin Rabi’a da kwashewa akwai kwamfuta, wacce a ka kiyasta kayan da ke cikinta sun kai darajar Naira miliyan 40. Bugu da kari, an shaidawa jami’an tsaron cewa, a cikin kayan lefen akwai shaddojin Gazna da atamfofi Sufa Holan, sannan akwai kananan kayayya da su ka kwashe wadanda iyayenta ba su kawo ta gidan da su ba, kamar tukunyar gas, na’urorin dumama daki, kafet-kafet da sauransu. Hatta kayan abinci da sabulai da kayan shayi sai da su ka kwashe.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 26 ga Maris ne Alkali Ibrahim Sarki Yola ya kashe auren, inda ya turasasa wa matar da ta biya mijin diyya bayan da lauyansa ya sanar da kotun yadda Rabi’a ta yi yunkurin kashe shi a lokacin da su ke tare, saboda ta gano ya na kokarin zai yi ma ta kishiya.
Haka nan kuma Barista Adamu ya sanar da kotun yadda matar ta zubar da juna-biyun da ke jikinta da kuma shan magungunan hana daukar ciki ta rika yi tun bayan da mijin nata ya sanar da ita cewa, ba zai bar ta ta yi aiki ba idan ta kammala karatun da ta ke yi a Jami’ar Bayero da ke Kano, saboda ya gano ta na tafiya wani waje daban da sunan ta tafi jami’a.
Ya kara wa kotun da cewa, asirinta ya tonu ne bayan da magungunan da ta ke sha su ka fara haifar ma ta da matsaloli, inda a ka kai ta asibiti, don duba lafiyarta. A can ne likitoci su ka yi bayanin cewa, ta samu matsala ne a mahaifarta sakamakon zubar da ciki da kuma shan irin wadancan magunguna da ta ke yi ba bisa ka’ida ba.

Wasu makotan iyayen Rabi’a, wadanda su ka nemi a sakaya sunansu, sun shaida wa wakilinmu mamakinsu kan yadda wannan lamari ya faru, sakamakon irin kulawar da mijin ya nuna wa Rabi’a tun kafin a yi auren, saboda ciwon da ta ke fama da shi, amma haka ya runtse idanu ya aure ta kuma ya yi ta dawainiya da ita har ta samu lafiya, sannan ya saka ta a jami’a, don ta cigaba da karatu.
To, a jami’ar ne abubuwa su ka lalace mu su, inda ta yi sababbin kawaye kuma ta hadu da wata kawa a unguwar da su ka fara zama. An tabbatar wa da wakilinmu cewa, yanzu haka ita ma waccan kawa mai suna Aisha aurenta ya mutu.

Haka nan binciken wakilinmu ya tabbatar da cewa, Rabi’a ta yi waccan jinya ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke birnin na Dabo kafin auren.

Yanzu dai mun saka na-mujiya mu ga shin tsohon mijin zai nemi hakkokinsa a gaban kotu ne ko kuwa, a’a, musamman ma saboda waccan na’rar kwamfuta mai dauke da wasu muhimman kayayyaki a cikinta na dimbin miliyoyin Naira. Wata majiya dai ta nuna, iyayen Rabi’a sun ci alwashin ba za ta dawo da abubuwan da a ke zargin sun sace ba, kuma za su yi amfani da wani kanin mahaifiyarta, wanda ma’aikacin shari’a ne, don ba ta kariya. Ma ji ma gani!

 

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram