Mata uku sun kai hari ofishin ‘yan sanda a Kenya

0 1

Click to subscribe my channel

Wasu mata uku sun kai wani hari da ake zargi na
‘yan bindiga ne a babban ofishin ‘yan sanda na
birnin Mombasa na kasar Kenya.
‘Yan sanda sun ce matan sun je ofishin ‘yan sandan
ne domin kai rahoton sace musu wayar salula,
amma sai suka daba wa ‘yan sanda biyu wuka, tare
kuma da jefa bom da aka hada da fetur.
An harbe harbe matan har lahira, yayin da aka
wuce da ‘yan sanda da suka samu raunin zuwa
asibiti.
A dan tsakamin nan, ana ci gaba da samun hare
hare a yankin mai teku na kasar Kenya, kuma da
yawa daga cikin hare haren, kungiyar Al-Shabaab
ke kai su.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Click to subscribe my channel