Masu Yin whatsapp zasu fara Biyan Harajin kullum

0 3

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Majalisar dokokin kasar Uganda ta amince da wata sabuwar doka wadda za ta fara cajan ‘yan kasar da ke amfani d
shafin sada zumunta na WhatsApp harajin shlillings 200
kimanin naira 20) a kullum.

Har ila yau za su fara biyan harajin cinikayyan da suka yi
ta wayar salula, wato kashi 1

cikin 100 na kudin da aka yi kowace cinikayya ta waya. Dokar za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yulin bana.

Sai dai wadansu ‘yan majalisa uku sun nuna adawarsu ga
sabuwar dokar, inda suka bayyana sabuwar dokar da “kara bar haraji kashi-kashi,” kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.

KARANTA WADANNAN;
1 of 2

Yan majalisa Robert Kyaggulanyi da Joshua Anywarach da kuma Silas Aogon sun ce karin haraji zai zama wani take ‘yancin masu amfani da WhatsApp saboda ana cajansu har aji kan katin wayar da suke saya.

Dan majalisar Arewacin Kasanda, Patrick Nsamba na jam’iyar adawa, ya ce:

“Abu ne mai sauki dan majalisa ya ce harajin kaso 1 cikin
100 kudi ne kadan, amma ga mutanen da suke samun kasa da dala a rana, kudi harajin kudi ne mai yawa.”

A galibin kasashen duniya ba a biyan haraji kafin amfani d
a kafar sada zumunta ta WhatsApp.

©hausazone

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram