Maryam Gidado Na kwance a Asibiti

0 363

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Maryam Gidado Na kwance a Asibiti, Shararriyar jarumar nan da tauraronta ke hasanakawa a masana’antar Kannywood, Maryam Gidado wacce akafi sani da Maryam Babban Yaro yanzu haka tana kwance a asibiti tana karbar kulawar likita sakamakon rashin lafiyar da take fama da ita.

Dandalin Kannywood: Wata fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na kwance a asibiti ba lafiya.


Maryam GidadoDuk da dai har yanzu ba’a san takamaiman abun da ke damun ta ba, amma dai tana cikin wani mawuyacin halin da take bukatar addu’a daga dukkan al’umma maza da mata masoyan ta.

Majiyar Arewaclass ta tuna cewa a baya jarumar ta yi tsokaci akan wani babi day a shafi rayuwarta inda ta bayyana cewa ita bazawara ce domin ta taba yin aure har sau biyu.

KARANTA WADANNAN;
1 of 38

Jarumar ta bayyana cewa anyi mata auren fari tana da shekaru 13 a duniya kasancewarta Bafulatanar asali.Maryam gidado

Ta kuma haifi ‘Yarta ta farko tana da shekaru 14 bayan shekara daya da aurar da ita ga mijin nata na fari.

Ta kuma kara yin aure inda anan ne ta haifi ‘Danta na biyu,sannan kuma ta bayyana cewa alokacin da take da cikin ‘Dan nata na biyu ne sai mijin ya gudu ya bar ta.

Source:presshausa

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram