Man United Na Tu nanin dauko Zidan

0 10

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Manchester United tana son tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya maye Jose Mourinho idan ya tafi, in ji sun.

Wasu rahotanni sun ce Manchester na iya raba gari da Mourinho, kamar yadda kocin ya nuna alamun shi ma zai iya ajiye aikinsa.

Inter Milan na sha’awar sayen dan wasan tsakiyar Real Madrid dan kasar Croatia Luka Modric, mai shekara 32, wanda yake hutu a Italiya, in ji jaridar Gazzetta dello.

Chelsea na fatan doke Real Madrid wajen takarar sayen dan wasan Bayern Munich dan kasar Poland, Robert Lewandowski, mai shekara 29, in ji,(Star).

Chelsea tana fatan cewar albashin fan 290,000 a ko wane mako da za ta rika biyan dan wasan tsakiyar Faransa N’Golo Kante, mai shekara 27, zai sa dan wasan Belgium Eden Hazard, mai shekara 27, ya tsaya. In ji (Evening Standard)

Har yanzuParis St-Germain ba ta hakura da bukatar karbo Kante ba, in ji (Mirror)

Tottenhamna son karbo dan wasan gaba na Crystal Palace Wilfried Zaha kan kudi £45m.

KARANTA WADANNAN;
1 of 3

Palace ta yi watsi da tayin farko da Chelseata yi kan dan wasan mai shekara 25, in ji (Sun)

Jose MourinhoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMourinho na fuskantar kalubale a Manchester United

Chelsea ba ta gamsu da dalilan Willian ba na kin dawo wa daga hutu saboda matsalar fasfo dinsa. Dan wasan mai shekara 29 wanda Manchester United da Real Madridsuka nuna sha’awar suna so har yanzu bai fara atisaye ba a Chelsea, in ji (times)

Barcelona tana son golan Liverpool mai shekara 30 dan kasar Belgium Simon Mignolet, in ji (Sky Sports).

Dan wasan gaba na Juventus Gonzalo Higuain ya amince ya koma AC Milan matsayin aro, kuma kungiyar na iya sayensa idan an kammala kaka kan £32m, in ji Guardian).

Real Madrid ta tunkari dan wasan Liverpool Mohamed Salah na Masar domin maye gurbin Cristiano Ronaldo wanda ta sayar wa Juventus, in ji (El Pais, via Star)

Tsohon dan wasan Arsenal da Faransa Thierry Henry ya amince ya zama sabon kocin Masar, in ji (King Fut, daga Talksport).

©bbchausa

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram