Mai kamfanin Facebook yayi Asarar Kudin da sukafi Na Dangote cikin kwana 2

0 9

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

A makon jiya ne Mark Zuckerberg wanda yana cikin manyan Attajirin Duniya ya rasa abin da ya haura Dala Biliyan 16 a cikin kankanin lokaci. Wannan kudi dai sun fi karfin Naira Tiriliyan 5.

A Ranar Laraba da ta wuce ne mu ka samu labari cewa Mark Zuckeberg ya rasa Dala Biliyan 17 a cikin kudin da ya mallaka a Duniya.

Duk da yawan wannan kudin dai ba su kai kashi 1 na 5 din abin da Matashin ya ke da su ba.

Hannun jarin kamfanin nan sada zumunta na Facebook nebya fadi kasa wanda ya sa ribar Kamfanin na bana ya ragu matuka.

Abin da Zuckerberg ya rasa sun haura gaba daya dukiyar Aliko Dangote wanda ya fi kowa kudi a Afrika Da kuma duk wani bakar fata a Duniya.

KARANTA WADANNAN;
1 of 2

Kwanakin baya da kasuwa tayi kyau Mark Zuckerberg ya samu Dala Biliyan 3 wanda idan aka yi lissafi zai haura sama da Naira Tiriliyan guda.

A lokacin nan sai da arzikin
Mark Zuckerberg ya doshi sama da Dala Biliyan 66.

Abin da Dangote ya mallaka dai bai wuce Dala Biliyan 12.

A daa dai kamin faduqar hannun jarin kamfanin nashi ‘Dan Matashin watau Mark Zuckerberg ne mutum na 3 a jerin kudi a Duniya amma bayan faduwar hannun jarin, sai ya
koma na 6. Jeff Bezos wanda ya ba Dala Biliyan 150 baya da Bill Gates duk sun sha gaban sa.

©arewatop

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram