Mahajjatan Nigeria Na fuskantar kallubale a saudia

0

Jaridar yanar gizo ta SaharaReporters ta
rawaito cewa Alhazan Nijeriya da a yanzu ke
jibge a Jidda na fama da lalurori daban-daban sakamakon rashin kulawa ta fuskar
lafiya da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta
Kasa, ta gaza
samarwa ga mahajjatan.

Majiyar da ke can Jidda ta fadawa Sahara
Reporters cewa, hukumar Hajji ta gaza
wajen samar da walwala ga mahajjata bayan
da ta yi wani makeken kari akan kudin
kujera.

Majiyar ta ci gaba da cewa mahajjatan
Nijeriya da dama yanzu haka na fama da
zazzabin ciwon sauro:
“Yau kwanana hudu ina fama da zazzabin
cizon sauro amma ban samu wata kulawa ba.
Na kai kuka na wajen jami’an gwamnati,
amma sai suka ce min na ci gaba da addu’a
ga Allah ya bani lafiya domin su babu wani
abu da
za su iya yi min sakamakon hukumar kula
da alhazai ta kasa da ta rike komai,”

“Mahajjatan Nijeriya da dama a yanzu haka
na kwance a asibitin Sarki Abdul Aziz ba
tare da wata kulawa ba.

KARANTA WADANNAN;
1 of 93

Tawagar jami’an kula da lafiya ta Nijeriya
ba sa bada wani tallafi na a zo a gani, sai
alkawari da suke ta yi mana na cewa za su
inganta ayyukansu.

” A cewar mahajjacin da ya sanar da kafar
Sahara halin da suke ciki a Saudiyya Wasu
mahajjata har sun farma ma’aikatan huku,ar
hajji ta kasa sakamakon rashin kulawar da
suke basu. Sai dai ma’aikatan sun bayyana
musu cewa ba a basu wadatattun jami’an da
za su iya kula da yawan mahajjatan Nijeriya
ba.

Source; arewaclass.com.ng