Ma aikatan majalisar taraya na gudanar da zanga Zanga

0

A yau ma’aikatan majalisun tarayya suka fara wani yajin aiki na kwanaki hudu, don jawo hankalin hukumomi don sun biya su hakkinsu da suke bi bashi, a makon da ya wuce ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar lumana a harabar majalisar, amma hakan bai biya bukata ba. Tun da sanyin safiyar yau Litinin ma’aikatan suka yi wa harabar majalisar kawanya, inda suka toshe duk hanyoyin da suke shiga majalisar, a cewarsu sun fara yajin aikin jan kunne na kwanaki hudu, wanda in ba a biya musu bukatun su ba za su shiga yajin aikin sai baba ta gani, tuni dai aka kai jami’an tsaro harabar majalisar saboda gudun samun hatsaniya.

KARANTA WADANNAN;
1 of 93

©ledershipayau