Ma aikatan Buhari sun fara taba kasa

0 1

Click to subscribe my channel

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin a kori tsohon shugaban kwamitin yin
garambawul ga shirin fanshon kasar,
AbdulRasheed Maina.

A wani sakon da aka wallafa a shafin Shugaban kasar na Twitter, Shugaba Buhari ya ce a kori
Abdulrasheed Maina daga aiki nan take, a kuma yi bincike game da yadda akayi ya koma aikin
gwamnati.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Kazalika, shugaban kasar ya ce umurci shugabar ma’aikatan gwamantin tarayyar Oyo-Ita Winifred Ekanem, ta mika rahoton binciken ga ofishin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa,
Abba Kyari, kafin a tashi daga aiki ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba 2017.

Wannan matakin dai ya biyo bayan matsin lamba daga ‘yan Najeriya da masu fafutuka suka yi n neman an cire mutumin da hukumar yaki da
masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC ke nema ruwa-a-jallo.

Click to subscribe my channel