Lamido ya fadi inda manya Barayin Nigeria suke

0 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wani tsohon gwamna, Sule Lamido yace jam’iyya mai ci na APC ta hau kan mulki ta hanyar amfani da karya

Tsohon gwamnan yace APC cike take da mutane masu aikata cin hanci da rashawa

Ya zargi shugaba Buhari da kare yan APC daga bincike.

Sule Lamido wanda yayi aiki a
matsayin gwamnan jihar Jigawa ya
zargi shugaban kasa Muhammadu
Buhari da kare mambobin jam’iyyar
APC.

A wani hira tare da jaridar Daily Trust, tsohon gwamnan ya zargi jam’iyyar APC day akin neman zabe akan karya domin su samu kuri’un mutane.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Lamido yace bai kamata a dunga son kai a wajen yaki da cin hanci da
rashawa ba.

Manyan barayi na a jam’iyyar APC – Sule Lamido Ya ce: “Idan kana tare da APC, Buhari zai wanke ka sannan kuma cewa wannan dalilin ne yasa dukkan mutanen da suka bar PDP suka koma APC suka kasance tsarkakaku.

“Idan suka kira mu barayi, kananan
barayi ne suka saura a PDP, manyan
barayin suna APC.

“Idan bazasu iya shugabanci ba, sun
ajiye aiki sannan mu kuma mu karba.”

©naijhausa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.