Kyauren jirgin sama ya fado a wani gida

0 3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Iyalan wani gida a Indiya sun shiga
halin firgici a yayin da kofar wani jirgin sama ta fado a kan rufin gidansu a birnin Hyderabad

Allah ya taimaki wani mutum da ke yi wa rufin kwanon gidan fenti ya tsira, don ya tafi cin abinci a lokacin da al’amarin ya faru.

Wani jami’in ‘yan sanda ya shaida wa sashen BBC Telugu cewa al’amarin ya faru ne a yayin da karamin jirgin mai daukar mutum hudu ke tafiya kasa-kasa a sararin samaniya.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Ya kara da cewa matukin jirgin da
wanda yake koya wa ma sun tsira,
kuma tuni aka kaddamar da bincike
don sanin ainihin abun da ya jawo
faruwar lamarin.

Wani sufeton ‘yan sanda Karan Kumar Singh, ya ce: “abu ne da aka saba gani jirgin koyon tuki na yawo kasa-kasa a sararin samaniya a wannan yankin.”

A watan Satumba ma wani matukin
jirgi da wanda yake koyawa sun sha da kyar inda suka tsira da jin raunuka a irin wannan al’amari, inda jirgin da suke ciki ya fadi a yankin na Hyderabad.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.