Kungiyoyi Sun Himmatu Wajen Kawar Da Matsalolin Da Suka Mamaye Arewacin Najeriya

0 3

Click to subscribe my channel

Yayin da aka shigo sabuwar shekara ta 2017, batun ilimin ‘ya ‘ya mata da
almajirai da kuma dakile yawaitar sake saken aure na daga cikin abubuwan da kungiyoyi da kuma cibiyoyin nazarin ci gaban al’uma sukace zasu sanya a gaba.

Batutuwan ilimi da ilimin ‘yan mata da almajirai da matsalar shaye-shaye da matasa ke yi, na daga cikin manyan matsalolin da
suka mamaye lardin Arewacin
Najeriya. game haka ne kungiyoyin
rajin ci gaban mata da yara kanana, da kuma cibiyoyin nazari da bincike kan harkokin rayuwar iyali ke shan
alwashin ribanya kokarinsu wajen
cimma muradunsu a wannan shekara ta 2017.

Daraktar cibiyar nazarin jinsin bil
Adama da inganta rayuwar iyali ta
jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Aisha Abdul Isma’il, tace a bana cibiyar na da tsare-tsaren cimma muhimmannmuradun da ta saka a gaba. Ta kara da cewa la’akari da yawa da kuma nauyin aiyukan da suka rataya a wuyan cibiyar, ya sanya take kokarin kulla kawance da sauran hukumomi da cibiyoyi don cimma nasara.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

A shekarar da ta gabata ne aka gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki kan kalubalen cin zarafin kananan yara dabmata, wadda cibiyar bincike kannlamuran dimokaradiyya ta Mambayya
a jihar Kano ta shirya.

Malama Hauwa Ibrahim El-Yakubu,
guda cikin wakilan da suka halarci
taron tace a wannan shekara ta 2017 hukumomi da kungiyoyi ya kamata su himmatu wajen aiwatar da abubuwan da taron ya cimma.

Click to subscribe my channel