Kungiyar kallon kafata ta matan Nigeria ta lallasa Zambia

0 76

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Kungiyar kallon kafan Nijeriya ta mata (Super Falcons) ta lallasa takwararta ta kasar Zambia da ci hudu da nema a filin wasa na Cape Coast a gasar cin kofin Nahiyar Afirka wanda ake bugawa a kasar Ghana.

Najeriya tayi rashin nasara da ci daya da nema a wasan ta na farko da ta buga da kasar Afirka ta Kudu wanda aka buga a ranar lahadin da ta gabata.

Oparanozie ce ta fara saka kwallo daya a raga kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Francesca Ordega ta jefa kwallo ta biyu.

Oparanozieta sake yin nasarar jefa kwallo ta uku a raga kafin daga karshe Amarachi Okoronkwo wadda ta shigo daga bisani a matsayin chanji ta jefa kwallo ta hudu.

A yanzu dai Nijeriya itace ta daya a rukunin B kafin kasar afirka ta Kudu su fafata da Equatorial Guinea a daren yau.

Super falcons zasu buga wasan su na karshe da Equatorial Guinea a ranar asabar mai zuwa.

KARANTA WADANNAN;
1 of 4

#leadershipayau

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram