Kudaden wanda basuyi BVN ba sun zama na gwamnati

0 3

Click to subscribe my channel

Kotun koli ta kasa ta baiwa gwamnati dama da a tattara mata kudaden asusan bankunan da ba’a yi musu BVN ba.

Shugaban lauyoyi na kasa, Abubakar Malami, ne ya shigar da wannan neman izinin da yawun gwamnati.

Ana kyautata zaton cewa wadannan kudaden a kalla sun kai biliyoyin Nairori, daloli, da fam-fam suna zaune a bankuna kawai ba’a amfani da su.

Kotun ta umarci duka bankunan kasa 19 da jama’a ke ajiyar kudi da su mika wa gwamnati sunayen kowanne asusun da ba’a yi wa BVN ba, da kuma nawa ne a ciki

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

A yanzu haka bankuna 16 sun baiyana za su tura, sauran ukun kuma sun yi gum. Ukun sune:
bankunan Unity, Wema da Zenith.

Gwamnati ta umarci duka bankunan da su buga sunayen masu asusan, da balas din da ke ciki, a jaridu, da kuma ba su sati biyu don su fito su
fadi lallai dalilin me ya sa bai kamata a baiwa gwamnati kudin ba.

Wannan batu na kotu ya sa shiyyoyi sun yi caa a kan gwamnati a kan bai kamata a tilastawa bankuna su baiyana abin da aka basu ajiya ba.

©hausa.naij

Click to subscribe my channel