Ko shinkafar Ebonyi zata iya ciyar da Nigeria?

0 2

Click to subscribe my channel

Matsalar tsadar abinci da ake fama da ita a
Najeriya ta sa gwamnatoci da dama sun farka daga
mafarkin da suke cewa man fetur zai iya rike su.
Tuni wasu jihohi da ma gwamnatin tarayya suka
ce sun fara daukar matakan inganta noma domin
ciyar da kai da samun kudaden shiga.
Sai dai wata jiha daya tilo da ake ganin ta yi nisa
wuirn bunkasa harkar noman shinkafa ita ce
Ebonyi, wacce wasu ke ganin za ta iya ciyar da
kasar baki daya.
Tun shekaru fiye da 50 da suka gabata garin
Abakaliki, babban birnin jihar da a yanzu aka fi
sani da jihar Ebonyi, da ke Kudu maso Gabashin
kasar.
Wani mataki da jihar ta dauka a baya-bayan nan
shi ne na hana shigar da shinkafar kasar waje
domin karfafa wa manoman gida gwiwa ba ya ga
sauran matakan da ta ke dauka.
Kwamared Sam Igwe, wani mataimaki na
musamman ga gwamnan jihar, ya shaida min
cewa baya ga illa ga manoman cikin gida
shinkafar ta waje na da hadari ga lafiyar jama’a,
inda ya yi zargin mutum biyu sun mutu bayan cin
shinkafar.
“Muna sa ran wannan mataki zai taimaka wurin
bunkasa noman cikin gida,” In ji Mista Igwe.
Sai dai jami’in gwamnatin ya ce, ba wai
dungurungum aka hana shiga da sayar da
shinkafar wajen ba.
“Ba za mu hana shigo da shinkafar ba, idan har
tana da ingancin duk da ya kamata, da takardun
da suka dace daga hukumar kula da ingancin
kayyaki ta Najeriya da shaidar biyan kudin fito,
kuma komai yana bisa ka’id, kafin a shigo da ita.
Mutum ya iya sayar da shinkafar ta waje.
Casar shinkafa
Ya kara da cewa za a dauki matakan kwacewa da
konawa idan aka kama mutane suna sayarwa ba
bisa ka’ida ba.
Don ganin wannan mataki na hana ssayar da
shinkafar wajen barkatai a jihar ta Ebonyi ya yi
tasiri, musamman gwamnatin jihar ta kafa wata
hukuma da ke sa ido kan batun.
Ga dubban manoman jihar Ebonyi dai, hana shigo
da shinkafar kasar waje da sayar da ita a duk
fadin jihar wani zancen ji ne, kuma abin farin ciki.
Domin hakan zai kara masu kwarin gwiwar yin
abin da suka kwashe shekaru aru-aru suna
gudanarwa a matsayin wata babbar sana’a, wato
noman shinkafa.
Daya daga cikin manoman Okotoka Ogbozogwu ya
ce yana noma hekta fiketa fiye da 40.
Ya kara da cewa “A hekta 18, na yanki fiye da
buhu 300, kuma ina ci gaba da yanka. A shekara
dai ina noma hekta fiye da 40 da damina kadai. Ba
ma noman shinkafa na rani, saboda rashin kayan
aiki,” in ji shi.
Sai dai yayin da wasu manoman ke amfani da inji
wajen fyade shinkafarsu, wasu kuwa ba su da
halin samun injin. Don haka, da hannu suke aiki,
kamar yadda na tarar da wani manomi rike da
sanda yana fyadin shinkafarsa.
Wani manomi mai suna Luke Udeh, ya ce “Ba
wanda ke tallafa mani da hannuna nake aikin
shinkafar, don haka a duk tsawon yini guda buhu
uku kawai nake iya fyadewa ni kadai. Da kamar da
inji ne abin da zan iya yi zai fi haka matuka.”
Wannan ne ma ya sa manoma ke neman tallafi, a
cewar Mista Ogbozogwu.
Ita dai shinkafar gida ba wai noma ta a fyade ta
zama samfarera ne matsalar ba, yadda za a cashe
ta, a fidda tsabarta tsaf-tsaf.
Mafi yawan masu aikin casar shinkafa a jihar
Ebonyi dai, manoman shinkafar ne, kuma mutane
irinsu Osulor Emmanuel, na ganin alfanun matakin
gwamnati na hana sayar da shinkafar waje.
“A da muna fama da kamfar masu sayen
shinkafarmu ta gida amma yanzu da yake
gwamnati ta dakatar da sayar da shinkafar waje,
muna jin dadi game da hakan. Kuma a shirye
muke mu samar da yalwatacciyar shinkafa daga
namu bangaren.”
Ba bambancin farashi
A kokarin kara ingancin shinkafar ta gida,
gwamnatin jihar Ebonyi ta kakkafa wasu wuraren
casar shinkafa irin na zamani har guda hudu a
sassan jihar.
Mutumin da ke kulda wurin casar Mista Ogbonna,
ya ce:”Nan ne muke casar shinkafa, mu sanya ta a
buhu, kuma a yanzu muna casa fiye da buhu dari
biyar a duk rana. Idan ma ana bukata za mu iya
cashe fiye da haka.”
Jihar Ebonyi dai, ta hau hanyar kai wa ga wani
mataki na bunkasa ta fuskar noma da casar
shinkafa, a cewar Kwamred Joseph Onunu,
manomin shinkafa, kuma shugaban kungiyar masu
casar shinkafa ta jihar.
“Yau muna da karfin samar da shinkafa mai yawa,
saboda muna da injinan casar shinkafa fiye da
1,500 mallakar jama’a masu zaman kansu.
Kuma a kullum muna samar tan 180, na buhunan
casassar shinkafa a cikin sa’o’i hudu. Idan ma muka sami karin masu yi mana ciniki za mu iya kara adadin da muke samarwa”.
Sai dai ra’ayin wani magidanci Onyemaechi Nzekwe ya ce akwai sauran aiki a gaban manoman:
“Na gwammace shinkafar waje fiye da ta gida, domin ta wajen tana ba ni duk abin da nake ra’ayi a shinkafa. Ga shi ba ta da tsakuwa, ga kuma dadi idan an dafa”.

Bambancin farashin shinkafar gida da ta wajen ba shi da yawa, domin ana sayar da babban buhun shinkafar gida naira 19,000, ita kuma ta wajen
naira 21,500.”

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Bisa ga dukkan alamu, wannan mataki da gwamnatin jihar Ebonyi ta dauka na hana sayar da shinkafar waje a yankinta, sannu a hankali yana samun tagomashi.
Har ma gwamnatin tarayyar Najeriya ta albarkaci
abin.

Wannan kam, wani kyakkyawan albishir ne, da ma kuma masu iya magana kan ce, ”Kowa da hannunsa yake tagumi”.

Click to subscribe my channel