Ko Man city Zata kafa tarihin Daukan Kofuna Guda 4

0 57

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Manchester City ta je gidan Fulham a wasan gasar Premier ranar Asabar din nan cike da sanin cewa wasa 15 ya rage ma ta da kafa tarihin cin kofuna hudu a kaka daya.

Bayan da tuni ta riga ta dauki kofin League, maki daya ne tsakaninta da Liverpool wadda ke mara ma ta baya a Premier, da kuma kwantan wasa daya, yayin da za ta fuskanci Brighton a wasan kusa da karshe na kofin FA, sannan kuma ta fafata da Tottenham a wasan dab da na kusa da karshe a gasar kofin Zakarun Turai.

Bugu da kari kuma masu fashin-baki na ganin kungiyar tana da dama da karfin cin dukkanin wadannan kofuna da ke gabanta a yanzu.

To amma za ta iya tabbatar da wannan hasashe kuwa?

Akwai wata kungiya da a tarihi ta taba samun irin wannan dama kuwa?

'yan Man United a kakar 1998-99, lokacin da suka ci kofuna uku a kaka daya

Kungiyoyin Ingila biyu ne kawai suka taba samun irin wannan dama ta cin kofuna hudu zuwa ranar 30 ga watan Maris: Chelsea a kakar 2006-07, da Manchester United a 2008-09.

Chelsea wadda a lokacin Jose Mourinho ke ma ta kociya ta kasance da wannan dama har zuwa 1 ga watan Mayu, kafin ta yi rashin nasara a bugun fanareti a karawarta da Liverpool a wasan kusa da karshe na kofin Zakarun Turai.

Shekara biyu bayan nan Manchester United karkashin Sir Alex Ferguson ta yi kokari har zuwa ranar 19 ga watan Afrilu, kafin ta gamu da karshen wannan fata, bayan da Everton ta yi waje da ita a bugun fanareti a wasan kusa da karshe na kofin FA.

KARANTA WADANNAN;
1 of 3
Riyad Mahrez ya ci wa Man City Tottenham 1-0 a Premier a watan Oktoba

Manchester United din harwayau ta kai matakin kusan daukar cin kofunan hudu, kafin ta sha kashi a hannun Barcelona a wasan karshe na cin kofin Zakarun Turai.

Bajintar da za a ce United din ta yi da ta fi kowacce a tarihinta ita ce ta cin kofuna uku daga cikin hudun a kakar 1998-99, amma ina ko alama ba ta kai ga kusan daukar hudun ba a wannan kaka, inda ta yi rashin nasara a hannun Tottenham a wasan dab da na kusa da karshe na kofin League ranar 2 ga Disamba.

Wata gwarzuwar kungiyar ta Premier, ita ce tawagar Arsenal da aka yi wa lakabi da ‘invincibles’ ta kakar 2003-04.

Tawagar ta kafa tarihin ganin ba wata kungiya da ta doke ta a wannan kaka a gasar Premier, amma burinta na daukar kofunan hudu a kaka daya ya zo karshe ranar 3 ga Fabrairu, lokacin da suka sha kashi da ci jumulla 3-1 da Middlesbrough a wasan kusa da karshe na kofin League.

Pep Guardiola na Manchester City

Tawagar Manchester City, wadda ta yi ta kawar da tarihin da aka kafa a baya a Premier a wajen yawan maki da kuma cin yawan kwallo, a kan hanyarta ta daukar Premier a bara, tana fafatawa a fagen daukar kofuna hudu har zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu, kafin ta gamu da rashin nasara a hannun Wigan a kasar cin kofin FA.

To amma babbar bajinta da City din ta yi kafin wannan shekarar ta kasance ne a kakar 2013-14, lokacin ta kungiyar karkashin Manuel Pellegrini ta sha kashi a wasan dab da na kusa da karshe na kofin FA ranar 9 ga watan Maris, harwayau a hannun Wigan. Saboda haka a iya cewa kungiyar ta ci sa’a da ba za ta hadu da Wigan din ba a bana.

Yanzu dai ba a san ko Manchester City za ta yi wannan bajinta da ta gagara ba a Ingila.


Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram