Ko kasan yaushe za a rufe biyan kudin aikin hajji na Badi a Nigeria

0

Hukumar aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta kayyade watan Mayu na shekarar 2018 a matsayin lokacin rufe karbar kudin kujerun aikin hajji na maniyyatan badi.

Hukumar Aikin Hajji ta kayyade lokacin rufe karbar kudin maniyyatan badi Shugaban hukumar Abdullahi Mukhtar
Muhammad ne ya bayyana hakan a
ranar Alhamis din da ta gabata a wani taro da hukumar ta gudanar wanda ya kunshi wakilan hukumomin alhazai na
jihohin kasar nan.

Ya ke cewa, an bukaci dukkan
maniyyatan aikin hajji na badi da su
tabbatar da biyan kudin kujerun su
kafin karshen watan Mayu na shekarar 2018.

Majiyar arewaclass ta ruwaito daga majiyoyin ta cewa hukumar cewa, dukkanin masu ruwa da tsaki das u tabbatar da kiyaye dokoki da tsare-tsaren da hukumar ta gindaya,
wanda zai inganta harkokin hukumar.

Domin shawara ko bamu labari,
tuntube mu a:

Journalist012@gmail.com

Ko

www.facebook.com/arewaclass

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

©naijhausa