ko dogara yana kuka sai ya sauka

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar
wakilan Najeriya, Abdulmumini Jibrin, ya ce dole ne
kakakin majalisar ya sauka daga mukaminsa ko yana
kuka ko yana murna.
Yakubu Dogara da sauran shugabannin majaliasar na
fuskantar matsin lamba kan zargin yin cushe a
kasafin kudin kasar na bana.
A ranar Laraba ne hukumar yaki da cin hanci da
rashawa ta EFCC ta fara gudanar da bincike kan
zargin, wanda Mista Jibrin ya gabatar mata, bayan da
aka kore shi daga shugabancin kwamitin kasafin
kudin.
Mista Dogara da sauran shugabannin majalisar sun yi
watsi da zargin da ake yi musu, suna masu cewa ba
su sabawa doka ba.
Abdulmumini ya shaida wa Yusuf Yakasai cewa ya yi
farin ciki da matakin na EFCC.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.