Kasar saudiya na neman maida aikatau aikin din-din

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A wani tsari da ya yi matukar kama da bautar da aka yi a zamanin mulkin mallaka, gwamnatin Saudi Arabia ta umarci bakin hauren da ke kasar wadanda suke aikin aikatau da kada su sake su bar ayyukansu. Masu aikin aikatau din a kasar ta Saudi Arabia na iya fuskantar tara da kora daga kasar, sannan a haramta masu kara shigowa har abada, matukar suka gujewa wadanda suka dauke su aiki, ko kuma wadanda suka tsaya musu aka dauke su aiki. Hukumar da ke kula da shige da fice ta kasar ta kuma haramtawa ‘yan kasar bada sabon aiki ga duk dan aikatau din da ya bar wajen aikinsa na da. Ta kuma yi masu barazanar fuskantar tara ko dauri a gidan yari idan har suka ki bin wannan doka. Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun jima suna Allah wadai da wannan tsari a sakamakon kamancecenuwar da ya ke yi da aikin bauta.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.