Kasan me zai faru da Buharin inzai tsaya takara A 2019??

0

Wani kungiyar siyasa watau Southern Mandate ta gargadi jam’iyyar mai mulki ta APC game da amincewa da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar jam’iyyar a shekara ta 2019.

Majiyar Arewaclass ta tabbatar da cewar, kungiyar ta ce ‘yan Najeriya za su yiwa shugabannin APC jefin shedan idan shugaba Buhari ya yanke shawarar neman shugabanci karo na biyu a zaben shugaban kasa na 2019.

A cikin wata sanarwa wanda shugaban kungiyar, Comrade Francis Ikonomwan ya sanya hannu, kungiyar ta bayyana cewa shugaba Buhari bai dace ya yi takara a zaben shekarar 2019 ba saboda ‘yan Najeriya ba su amince da shi don
ya cika alkawuransa ba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Ikonomwan ya ce maimakon tunani yin takara a shekara ta 2019, shugaba Buhari ya mayar da hankali a kan yadda zai cika alkawurran yakin neman zabe ga ‘yan Najeriya kafin karshen wa’adin mulkinsa.

“Ko da shugabannin siyasar da mutanen da suka yi gwagwarmaya a yakin nema zaben domin samun nasara a matsayishugaban kasar yanzu haka ya yi watsi da su duka ”,  Ikonomwan.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Ya ce, ” Idan APC ta amince da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa a shekara ta 2019, muna tsoron cewa ‘yan Najeriya na iya muna jefin shedan a yakin neman
zabe. Za mu iya ba jam’iyyun adawa
damar samu nasara a zaben shekara ta 2019”.

“Duk da haka, muna so mu kira shugaba Muhammadu Buhari don kada ya yi watsi da wannan kira kamar yadda ba son al’ummar Najeriya ba ne ya fito takara”.

“Abin da yafi muhimmanci ga shugaba Muhammadu Buhari yanzu shine ya kamata ya mayar da hankali yadda zai yi amfani da sauran wa’adin gwamnatinsa
don cika alkawuran da muka yiwa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe” inji shi.

©naij