Kasan innane yafi ko ina samun kaso mai tsoka a kasafin kudin bana

0 2

Click to subscribe my channel

Najeriya ta bayyana kasafin kudinta na 2018, wanda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke fatan zai samar da yanayin cigaba daga halin
karayar tattalin arzikin da take fama da shi.

Shugaba Buhari ya bayyana kasafin kudi na Naira tiriliyan 8.6 a gaban majalisar kasar, wanda ya ce zai samar da ayyukan yi ga matasa da kuma sabbin gine-gine a kasar.

A bana ne Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin arziki bayan faduwar farashin man
fetur, a shekarun baya-bayan nan.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya ce Najeriya: “ba za ta yi sakacin komawa cikin rikice-rikicen da suka addabi kasar a shekarun
baya a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ba.

Kasafin na bana ya zarce na bara da karin kaso 16 kuma gwamnatin Najeriya ta ce za ta mai da hankali wajen samar da hanyoyi da kiwon lafiya da gidaje da kuma samar da ayyukan yi.

Jadawalin manyan ma’aikatun da suka samu kaso ma fi yawa a wannnan kasafin kudin na 2018 ya nuna cewa ayyuka raya kasa ne ke kan gaba.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Amma ana sa ran gibin dake tsakanin kasafin kudin shiga da ainihin wadanda zasu shiga lalitar
gwamnati zai ragu daga Naira tiriliyan 2.005 wanda raguwa ce idan aka auna da na bara wanda ya kai naira triliyan 2.36.

Kasafin kudin dai zama doka ne kawai idan ‘yan majalisar kasar suka amince da shi.

Bangaren gwamnati da na majalisa sun sha kai ruwa rana kan kasafin kudi musamman wanda ya gabata, al’amarin da har ya kai ga tonon silili tsakanin ‘yan majalisar.

©bbc

Click to subscribe my channel