Karanta yadda wata yarinya ta dawo gida baya shekara biyu da mutuwar ta

0 39

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Wata yarinya da aka tabbatar da mutuwar ta, ta dawo gida bayan shekara biyu.

Iyayen yarinyar sun shiga halin dimuwa bayan yarinya ta dawo gida tare da shiadawa iyayenta cewar an binne itace ne a madadin ta.

An fara gudanar da bincike domin tabbatar dabgaskiyar labrin da yarinyar ta bayar

Dangin wata yarinya da ta dawo gida bayan mutuwar ta
da shekaru biyu sun shiga halin dimuwa da mamaki.

An bayyana cewar yarinyar ta mutu shekaru biyu da suka
wuce a garin Ndola dake kasar Zambia bayan ta sha fama da rashin lafiya.

KARANTA WADANNAN;
1 of 96

Rahotanni sun bayyana cewar an kai gawar yarinyar mai
suna Winnie dakin ajiyar gawa na wani asibiti kafin daga bisani a binne ta a wata makabarta dake Mitingo.

Sai gashi yarinyar ta dawo gida bayan shekaru biyu da mutuwar ta tare da shaidawa dangin ta da jama’a dake
cikin halin kaduwa cewar, an binne itacen ayaba ne a
madadin ta a lokacin da aka bayyana cewar ta mutu.

Wakilin mu ya bayyana mana cewar an gayyato jami’an ‘yan sanda domin binciken wannan abun mamaki.

Dangin yarinyar sun bukaci a gudanar da gwajin kwayoyin halitta a kan yarinyar.

Hukumar ‘yan sanda ta bukaci a gabatar mata da takardun shiadar haihuwa da na mutuwar Winnie domin cigaba da bincike.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram