Karan ta Littafin sanadin so part 1

0 53

Click to subscribe my channel

***SANADIN SO***
Part Oneoirf ranar TALATA da yammaccin ranar, Sararin samaniya ta dau gajimare gunduma-gunduma,

babu abinda zakaga yana yawo a sararin samaniyar face gajimar tare da tsintsaye suna ta shawagi.

Hakan yasa mutane da dama suke qoqarin komawa gidajensu domin kuwa bisa alamu ruwan sama za ayi.

Yan kasuwa da kuma ma’aikatan gobnati tare da yan zauna gari banza kowa yana gudu domin ya
isa gida tun kafin ruwan sama ya masa duka.

To nima dai ba a barni a baya ba domin kuwa nima agaggauce nake domin na koma gida saboda kada ruwan sama yamin na jaki wato ya
dakeni.

Ina gudu haka na isa gida kuma direct dakina na nufa, da zuwana cikin dakin, na zauna a akan kujera
domin huce gajiyar gudun da nayi, bayan nadan huta kadan haka yasa nayi yunqurin canza kayan dake jikina saboda gaba daya ya fara jiqewa da yayyafin ruwan saman, jim kadan da canza kayana, nayi tsalle na fada kan tsohuwar katifata
wacce aqalla shekararta goma ina kwana akai duk tabi ta tsufa ta dawo kamar tabarma, hakan
yasa naji na bugi qasa a daidai lokacin danyi tsallen na fada kan katifar.

Ko minti daya banyi ba da fadawata katifar, naji qararrawar wayata tana ringing da alamadai wani ne keson magana dani, hakan yasa na yunqura domin dauko wayar, banyi mamakin wanda ya kirani ba lokacin da naga ashe abokina Musa mai
waqa ne ya kirani domin mugaisa, bayan na amsa wayar sai naji wata sanyayyar murya tana rankado min sallama irin ta addinin Islama.

Da sauri na kawar da wayar daga kunnena domin kuwa ni a zatona abokina bashi da ko budurwa balle nayi tinani hadamu zaiyi da ita mu dan gaisa.

Sake duban screen din wayana nayi a karo na biyu domin tabbatar da wanda ya kirani ko da na sake dubawa sai naga musa din ne dai.

Abun yayi mutuqar bani mamaki haka dai na sake kara wayar a kunnena, na amsa sallamar da akamin tun a farkon dagawar da nayi.

“Hello” ta sake fada cikin sanyayyaar muryar tata wacce idan kaji muryar kai kace busar sarewa
ake.

“ni budurwar abokinka musa ce kuma nice wacce yake burin aura, shi ya bani numbarka domin na
kiraka mu gaisa” yarinyar nan tafadamin haka acikin wayar daga bisani kuma nima na mayar
mata da amsa kamar haka ‘Allah sarki gaskiya nagode sosai, kuma ina muku fatan alkairi Allah ya barku tare, na fada mata haka ta cikin wayar fuskata ta ciki maqil da tsananin mamakin akan cewa wai abokina musa mai waqa ya fara
soyayya mu kuma an barmu a baya.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Haka dai muka gama gaisawa harma nace da ita yanxu ina abokin nawa yake ? Gashi nan kusa dani ta fada cikin karyaryiyar murya kamar xatayi kuka, hmm lallai mata sai Allah na sakeyin irin wnan tinani a karo na biyu.

Snan nace da ita bashi wayar nan dai shima muka gaisa har ma nake tambayarsa ya Kaduna dafatan dai yanajin dadin zama acen, daga bisani kuma na katsar da
wayar.

Bayan na katsar da wayar, sai na fara nazarce zanarcen irin wanda na saba a duk lokacin da na kwanta akan tsohuwar katifata, a irin wnan
nazarin ne ma na nazarto labarin da ya gabata da kuma na baya cen wato labarin QUEEN HAFSAT da kuma MURADIN RAINA..

Banyi wani mamaki ba lokacin da wannan labarin wanda kake karantawa yanxu ya fadomin cikin
tinanina, domin kuwa inhar zan kwanta akan katifata to yanxu xanyi nazari da tinanin qirqirar labari.

Tun da nashigo dakin ruwan sama ake kamar da bakin qwarya har lokacin da mukayi waya da
budurwa musa, aqalla an dauki kamar awa biyu ana kwantama ruwa babu qaqqautawa daga
bisani kuma ruwan saman ya tsaya…

Bayan dauke ruwan saman da akayi hakan ya tilastamin fitowa domin gabatar da sallar ibada kuma tare da cin abincin dare, ban bata wani
dogon lokaci ba na kammala duk abinda ya dace..

Allah sarki a wannan karan kuma tinanin Abokina bilya nake da khadeeja wadanda suka yaudareni
kuma sukaci amanata acikin labarin da ya gabata wato muradin raina shi ne ya fado cikin xuciyata adaidai lokacin na qara tsalle na fada kan
tsohowar katifar tawa.

Jim kadan da fadawa kan tsohuwar katifata sai najiyo dan sautin kuka yana tashi daga waje………………

Mu hadu a kashi na biyu ©kader Adam journalist

Hakin mallakap da kuma kirkira matashi Kaader adam

Click to subscribe my channel