Kambun Man City Yadawo Gareta

0 22

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Gabriel Jesus ya ce zuwan mahaifiyarsa Ingila ya taimaka masa gaya wajen buga wasa bayan da ya taimaka wa Manchester City kwato kambunta daga hannun Liverpool.

Gabriel Jesus ya shafe minti 487 bai zura kwallo ba a gasar Firimiya tun watan Agusta – wanda ke nufin ya shafe wasanni 11 ko mintune 487 kenan – amma sai ga shi ya zura kwallo biyu kafin Raheem Sterling ya kara ta uku.

Dan asalin Brazil din wanda ya sanya hannu a kwantaragi da City a 2017 ya tsawaita zamansa a kungiyar har 2023.

KARANTA WADANNAN;
1 of 95

Mahaifiyarsa kuma ta dawo Ingila domin zama tare da shi.

“Na kara samun karfin gwuiwa saboda iyalina na tare da ni,” inji dan wasan mai shekara 21 da haihuwa.

Manchester City za su rike wannan kambun nasu na a kalla kwana guda ne kawai kafin wasan da Liverpool ke fatan doke Manchester United a filin wasanta na Anfield a ranar Lahadi da karfe 4 agogon GMT wanda zai ba ta daman sake kwace kambun daga hannun City.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram