Kalli yadda wata Mata tayi karar mahaifanta saboda sun haifeta mummuna

0 11

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Annabelle Jefferson, wadda ta ce ita mummuna ce Wata mata ‘yar jihar California a Amurka, Annabelle Jefferson, mai shekaru 44, ta maka iyayenta a kotu da kuma tana neman kudi dala milyan biyu sakamakon
haihuwarta da suka yi mummuna.

Jefferson, ta ce, iyayenta ne sanadiyyar rabuwar auren da take samu daga gidajen aurenta, a yanzu haka ta yi aure har sau uku amma muninta yake janyo ma ta sakin auren daga masoyanta bayan sun yi auren, tare da haddasa ma ta wasu matsalolin zaman aure.

“Tun da yake duk iyayena munana ne bai kamata su bari har su haihu ba, ya kamata gwamnati ta fito da wani shiri a kan ma’aurata masu muni, ko kuma ta dakatar da su daga
samun haihuwa baki daya,” cewar Jefferson.

Jefferson, ta kara da cewa, duk na dora alhakin rabuwar aurena a kan iyayena da kuma sauran matsalolin zaman gidan aure.

KARANTA WADANNAN;
1 of 6

A rabuwar aurena na farko tsohon mijina ya fada wa
alkali cewa, kullum da safe idan ya kalli fuskata sai
ya ji tashin zuciya har sai ya yi amai, wannan munin na matukar janyo min matsala
tsakanina da maigidana.

Rabuwar aurena da maigidana na karshe shi ne, kafin mu yi aure bai gani sosai, amma lokacin da aka yi masa tiyatar ido da mako daya kacal bayan ya fara gani sosai kawai sai ya ce, ya gaji da zama da ni, nan take ya sallame ni.

Jim kadan, dai sai Jefferson, ta fara shirin kafa kungiyar
masu irin matsalarta, da suka kai karar iyayensu gaban kuli’a.

kuma a yanzu haka ta fara mika koken nata ga jami’an gwamnati don ‘yan majalisar su
tatttauna a kan yadda batun zai zama doka, saboda dokar za ta iya sa a daina haifar munana da za su cigaba da fuskantar irin wannan matsalar.

©aminiya
.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram