Jonathan na Amfani da Avenger Wajen Hargitsa Gwamnatin Buhari – MEND

0 4

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiya mai rajin neman ‘yancin yankin Niger
Delta “MEND” ta bayyana cewa, tsohon shugaban
kasa Goodluck Jonathan ya daukai nauyin
kungiyar ‘yan tada kayan baya ta Niger Delta
Avengers domin ya hargitsa gwamnatin shugaban
kasa Buhari.
Ta fadi haka ne a wata sanarwa da ta fitar a jiya
Talata mai dauke da sa hannun wani Jomo
Gbomo, wacce ke da nufin yin watsi da musalta
batun daukar nauyin da tsohon shugaban kasar
ya yi.
MEND ce takardar da tsohon shugaban kasar ya
fitar da ke musalta batun ya yi matukar bata
haushi musammam ma kokarin karkatar da akalar
al’amarin da ya yi na cewa Henry Okah na
kokarin hallaka shi.
Kungiyar ta kuma ce zargin na kungiyar avengers
ya jaddada zaton da ta ke yi wa Jonathan din da
shi da mukarrabansa da suka fadi a zaben
shekarar 2015 na yin amfani da kungiyar wajen
lalata gwamnatin Buhari.
A farkon satin nan ne dai wani sashe na kungiyar
Niger Delta Avengers ta fitar da sanarwar da ke
zargin tsohon shugaban kasan da shi da wasu
gaggan ‘yan siyasa a yankin na Niger Delta da
daukar nauyin ta.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.