Jirkin yaki da yan Boko Haram yayi Hatsari

0 0

Advertisement

Jirgin yaki da yan boko haram yayi hatsari

Rundunar sojin sama ta Nigeria ta ce wani jirginta mai saukar angulu kirar Mi-17 da ke yaki da mayakan Boko Haram ya yi hatsari a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa, kakakin rundunar sojin
saman AVM Olatokunbo Adesanya ya ce
hatsarin ya abku ne ranar Litini kuma jirgin ya yi matukar lalacewa.

Sai dai rundunar sojin saman ta ce babu
asarar rai a hatsarin.

Sanarwar ta kara da cewa babban hafsan
sojojin sama na Nigeria Sadique Abubakar, ya bada umurnin kafa kwamitin bincike don gano musabbabin hatsarin.

KARANTA WADANNAN;
1 of 232

Kakakin rundunar sojin saman ya ce kafa
kwamitin ya yi daidai da tsarin da ake bi a kasashen duniya.

Rundunar sojin sama ta kuma bukaci hadin kai daga jama’a a kokarin ta na samar da tsaro da kare dukiyoyin ‘yan kasar.

©bbchausa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.