Jaruman kannywood goma da suka haska a 2016

0 29

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne muka
kawo muku jerin sunayen jarumai mata da
suka fi haskawa a shekarar nan ta 2016.

A yau kuma muna tafe da jerin jarumai maza.

Mubarak Umar na Jaridar Leadership Hausa ya yi nazari na musamman ta hanyar duba da
rawar da kowanne jarumi ya taka a finafinan da suka fito a 2016 a kowanne bangare da suka hada da jarumta, barkwanci da sauransu.
A yi karatu lafiya.

1- Sadiq Sani Sadiq
Wannan jarumi cikin ‘yan shekaru yana taka
rawar da yake tserawa tsara a tsakanin
takwarorinsa, musamman yadda yake iya juya
kansa zuwa siffofi daban-daban a cikin
finafinai.
Matsayin da ya fito a Kurma cikin shirin DAN KURMA ya kayatar matuka. Yadda yake
magana tamkar wanda ya yi a karatu a
makarantar kurame, lamarin akwai ban
mamaki. Kullum jarumin yana kokarin ganin
ya zo da wani sabon abu wanda masoyansa
ba su saba gani ba.
Dan Kurma shiri ne na barkwanci, wanda
Sadik suka fito tare da jaruma Hafsa Idris
(Barauniya). Masu sha’awar kallon finafinan
Hausa musamman na barkwanci sun yaba
sosai da rawar da jarumin ya taka.
A kullum yaumin jarumi Sadik na amfani da
wani irin tunani wajen zabawa kansa rol din da
zai fito a ciki. Ba ya duba tsadar kudin da za a
ba shi, illa iyaka wane matsayi zai fito.
Wannan na daga cikin manyan dalilin da suka
sanya a ‘yan shekarun nan jarumin yake lashe
manyan kyautuka a yayin gudanar da gasar
karrama jaruman Kannywood

2- Nuhu Abdullahi
Babu shakka yanayin da jarumin ya fito a cikin
Fim din FURUCI ya gamsar da kaso 90 cikin
100 na mutanen da suka yi sharhi a kai.

Hakika Nuhu ya nunawa duniya cewar lallai ya
kawo karfi da zai iya yin gogayya da manyan
jaruman Kannywood. Yadda ya bayyana a
matsayin dan tasha, ba shi da tsoro, duk abin
da zai da karfin zuciya yake aikata shi. Yayin
da mutum yake kallo, yana iya mancewa fim
ne ko kuma gaske.
Bayan nasarar da ya samu na shiga sahun
jaruman da ake labarinsu sakamakon rawar da
ya taka a fim din Furuci,

Nuhu Abdullahi ya
fara haskakawa a finafinan Turanci, wanda
labaransa ke da alaka da zamantakewar
rayuwar Hausawa.
Finafinan Turanci guda uku da ya fito a ciki,
THERE IS A WAY, LIGHT AND DARKNESS da
kuma THORNY, sun kara tabbatar da cewar
shekarar 2016 ta zo wa jaruman da babbar
nasara, ta yadda ba zai iya mantawa da ita ba.

3- Isah Adam
Jarumin BASAJA GIDAN YARI , wanda
bayyanarsa ta sauya yanayin shirin baki
dayansa, ya samu nasarar darewa sahu na uku
sakamakon rawar da ya taka a cikin wannan
shiri.
Yanayin da ya fito na babu sani babu sabo a
tsakiyar manyan jarumai ya birge manazarta
matuka. Zuwa yanzu za a iya cewa jarumin
bai taba taka rawa irin ta Basaja Gidan Yari
ba.
Fitowarsa ta kara daga kima da darajar fim
din, musamman da ake ganin sa matashi,
kyakkyawan jarumi mai cikar zati. Idan har
Isah ya ci gaba da taka rawa irin wadda ya yi
a Basaja, babu shakka nan da ‘yan wasu
kwanaki zai shiga sahun manyan jarumai da
ake labarin su a Nijeriya.

4- Ali Nuhu
Sarki Ali, kamar yadda masoyansa suka yi
masa lakabi, ba ya bukatar dogon bayani
game da yadda yake jan zarensa a
masana’antar shirya finafinan Hausa, watau
Kannywood. Gwani ne da aka hakikance cewar
batu na aktin a jikinsa kullum karuwa yake yi.
Rawar da ya taka a fim din UMAR SANDA,
wanda darakta Kamal S. Alkali ya bada
umarni, ya zo da wani irin salo da ya birge
‘yan kallo. Bayyanar damuwa a fuskar Ali
Nuhu a cikin shirin, da kuma yadda ya
kasance namijin duniya mai yadda da kaddara
a duk lokacin da wata musiba ta fadawa
mutum. Nuhu ya kara tabbatar wa da duniyar
finafinai shi din kwararre ne da kwanyarsa take
ja.
Wani masani da ya yi sharhi kan fim din ta
wayar tarho ya ce, “Akwai bukatar duk dan
Nijeriya musamman jami’an tsaro su kalli fim
din Umar Sanda, domin cike yake da sako mai
matukar ma’ana.

5- Adam A Zango
Tabbas rawar da Jabir (Adam A. Zango) ya taka a shirin Basaja GIDAN YARI abin yabawa
ce, domin idan kana son gane wane ne Zango
a fagen aktin, to ka kalli Basaja. A ciki ne yake
nunawa duniya cewar shi din cikakken jarumi
ne da duk masana’antar da ya kasance a
cikinta za ta yi alfahari da shi.
Zango yana amfani da kwarewa matuka
musamman a yayin da yake magana ko motsi
a cikin fim din Basaja. Ko idonsa ya motsa, dan kallo yana iya gano me yake shirin faruwa
ko kuma abinda yake nufi. Hakan na
kasantuwa saboda nakaltar labarin da ya yi tamkar a gaske abin yake faruwa.
Haka zalika fim din MIJIN BIZA da ya fito a matsayin matashin mayaudari, ya dace da rol
din matuka. Kayan da yake sanyawa, tafiyarsa
da maganarsa sun fassara wane ne shi.
Motsin jikinsa kawai abin yabawa ne.

6- Rabi’u Rikadawa
Zakulo fim guda a yi magana a kansa zai yi
matukar wahala, domin Rikadawa jarumi ne
cikakke da ya kware wajen sarrafa basirarsa ta
fuskoki da dama.
Jarumi ne da ba ya shakkar karbar rol kowane
iri ne, ya iya taka rawa kala-kala domin birge
‘yan kallo. Gwani ne da hatta turawan BBC
sun sallama masa a fagen aktin.
A cikin fim din Zinaru an ga yadda ya fito a
dan wiwi, kai ka rantse da ma can yana sha.
Yanayin tafiyarsa, maganarsa da motsinsa ya
yi matukar dacewa da yadda ‘yan wiwi suke
yi.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

7- Yakubu Muhammad
Fim din Turanci mai suna SONS OF THE CALIPHATE, na cikin jerin finafinan Yakubu ba
zai manta da su ba a rayuwarsa ta duniyar
nishadi. Duk da cewar shirin an yi shi ne da
harshen Turanci, amma hakan bai hana Fim
din mamaya a Arewacin Nijeriya ba.
Yakubu Muhammad ya fito a dan gidan attajiri,
wanda ba ya shakkar murza Naira a kasa.
Rawar da ya taka ce ta sanya shi zamowa
cikin wannan jeri a matsa yin na bakwai.
Kasancewar fim din Sons of the Caliphate yana
bada labarin yadda ‘ya’yan masu fada a ji ke
tafiyar da rayuwarsu musamman a Arewaci, ya
sanya aka zakulo jarumai irin su Yakubu daga
Arewa. Labarin kacokan kan yanayin rayuwar
‘ya’yan sarakuna ne da masu hannun da
shuni.
Zubin tsarin shirin na rayuwar Hausawa ne da
yanayin shugabancinsu, bambancin guda daya
tak kawai da aka yi shirin da harshen Turanci.
8- Sulaiman Bosho
Idan ana batun finafinan ban dariya a
masana’antar finafinan Hausa a yanzu babu
kamar sa. Duk ta inda aka bullo sai ya bulle
domin ya nishadantar da ‘yan kallo.
Fim din HEDIMASTA da Sulaiman Bosho ya
fito a matsayin Shugaban Makarantar furamare
ya bawa mutane dariya matuka. Yadda ya fito
a jahilin malamin makaranta, bai san bihim ba,
ko wani abu da ya danganci ilmin boko, amma
ya yi kane-kane tamkar wani farfesa a jami’a.
Salon barkwancin da ya fito da shi ya rage wa
masoya kallon finafinan Hausa radadin
rasuwar Rabilu Musa Ibro shekaru biyu da
suka gabata.
Bosho ya taka rawa a shirin Hedimasta, ya
nishdantar da masu sha’awar kallon finafinan
Barkwanci da harshen Hausa matuka.

9- Ramadan Booth
Rawar da ya taka a cikin fim din SAPEENAH,
wanda babban darakta Sunusi Oscar 442 ya
bada umarni, ta shiga sahun tarihin jarumin.
Hakika Ramadan ya yi amfani da kwarewa
matuka wajen nuna kansa a fagen aktin.
Har ila yau, GWARZON SHEKARA , fim ne da
yake bada labarin yadda wani matashi
(Ramadan) ya kamu da tsananin son jarumin
fim, watau Ali Nuhu. Ya kasance ba ya bibiyar
komai in ba labarin jarumin ba, inda yake
wasa da duk wani abu da ya shafe shi.
Ramadan ya taka rawa da za ta birge mutane
a cikin wannan fim, domin ya fito ne da wata
irin fuska da ba taba ganisa ba. Duk da cewa
fim din bai fita kasuwa ba, amma manazarta
sun zuba ido domin ganin yadda za wanye ta
cikin wannan shiri.

10- Abdul M. Shareef
Tallar fim din JANI MU JE kadai da ta fita a
shekarar nan ta rikita masu kallon finafinan
Hausa. Rawar da jarumin ya taka ta gwarzon
namiji, da ya tsinci kansa a tsakiyar abokan
gaba, mugaye da suke yunkurin zaluntar wata
budurwa.
Abdul ya yi amfani da matakin karfin tuwo
wajen kwato yarinyar daga hannun Basawa.
Yanayin yadda yake tayar da kwanji tamkar
wani dan dambe akwai kayatarwa matuka.
Yana cikin jaruman da ake yi masu
kyakkyawan fatan nan da ‘yan wasu kwanaki
zai shiga sahun wadanda ake damawa da su.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram