Jarabawar Da muka bawa Buhar ba Asalin Tasa Bacce

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Hukumar WAEC ta tabbatar da cewa Buhari ya rubuta jarrabawa a 1961 Hukumar ta WAEC ta ce takardar da ta mikawa Shugaba Buhari ba asalin sakamakon jarrabawar sa bane, WAEC tace idan mutum ya rasa ainihin sakamakon sa ne sai ya aika wasika domin a ba sa irin wannan takardar idan akwai bukata.

WAEC ta shafin ta na Tuwita ta nuna cewa abin da ya sa ba a ga sunayen wasu kwas-kwasan sun fito a takardar Shugaban kasar kamar yadda aka gani a baya ba shi ne ba a kawo jerin sunayen jarrabawar da ba a ci ba a irin wannan takarda.

KARANTA WADANNAN;
1 of 89

A wannan takardar da aka mikawa Shugaban kasa Buhari, babu sakamakon wasu ma’du’an irin su lissafi da sauran su.

Hukumar ta WAEC ta tabbatar da cewa babu fa shakka cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zana jarrabawar.
A game da hoton da aka gani na Buhari a jikin takardar, WAEC tace tana aiki ne da tsohon hoton da aka kawo mata idan ana neman sakamakon jarrabawar da ya bata.

WAEC din ta kuma ce a 2015 Buhari bai nemi a binciko takardun na sa ba.

Har wa yau wasu sun koka da yadda aka biyo Shugaban kasar har fadar sa aka mika masa takardar ta sa inda Hukumar tace tayi haka ne a matsayin Buhari na Shugaban kasa domin a ba sa girman sa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.