Jamus ta doke Nigeria da ci 2:0

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tawagar matasa ‘yan kasa da shekara 23ta Nigeria ta maza ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Jamus a ranar Laraba.Kasashen biyu sun fafata ne a wasan daf da karshe a gasar kwallon kafa a wasannin Olympic da ake yi a Brazil.Jamus ta ci kwallon farko ta hannun Lukas Klostermann a minti tara da fara wasa, sannan Nils Petersen ya kara ta biyu daf da za a tashi daga fafatawar.Da wannan sakamakon Jamus ta kai wasan karshe za kuma ta kara da Brazil wadda ta ci Honduras 6-0.Nigeria kuwa za ta kece raini a wasan neman mataki na uku da Honduras.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.