Isis tana fushi da Boko Haram Saboda kasa kafa Daular islam Nigeria

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Advertisement

Kungiyar ta’addanci na kasa da kasa, Islamic States West African Province (ISWAP-ISIS) tana shirin korar Boko Haram daga cikin ta domin ta gaza kafa daular musulunci a yankin arewa maso gabashin Najeriya kamar yadda wata rahoton ta bayyana.

Binciken da kungiyar sanya ido a kan ayyukan ta’addanci na kasa da kasa (ITMG) ya bayyana cewar an bawa kungiyar Boko Haram wa’addin shekaru uku su kafa daular musulunci a Najeriya. Sai dai ITMG ta ce ISIS tana gab da raba jiha da kungiyar Boko Haram saboda gaza kafa daular musuluncin cikin wa’addin da aka diba mata.

ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya , Rahoton na ITMG ya ce: “ISIS tayi barazanar korar Boko Haram saboda sun bari sojojin Najeriya sun kwace garuruwan da suka da ikon a kansu a baya kamar Camp Zero da ke dajin Sambisa da garuruwan Kukawa, Baga da yunkunan tafkin Chadi da kasar Nijar.

Har ila yau, rahoton ya ce akwai yiwuwar Boko Haram ta zo karshe kenan saboda galibin tallafin makamai da sauran kayan yaki da take samu yana zuwa ne daga ISIS.

“Cikin yarjejeniyar da Boko Haram su kayi da ISIS shine samun makamai.

KARANTA WADANNAN;
1 of 88

Yanzu za a yanke basu tallafin makaman wanda hakan na nufin karshen kungiyar ya zo kusa.

” Rahoton ya kara da cewa sabbin hare-haren da mayakar na kungiyar Boko Haram suke kaiwa kwana kwanan nan ba zai rasa alaka da wa’addin da aka basu ba barazanar korar su daga ISIS muddin ba su kafa daular musuluncin ba.

“Daya daga cikin dalilin da yasa ‘yan ta’addan ke tsananta hare-hare shine yana da nasaba da babban zabe mai zuwa, idan hare-haren ya tsananta hakan zai sa ba za ayi zabe a yankin ba. Amma a halin yanzu, Boko Haram ta gaza kwace iko a kan ko wanne gari a shekaru uku da suka gabata ba kamar yadda suka kwace kananan hukumomi 16 ba a yankin arewa maso gabas a zamanin gwamnati na baya,” inji rahoton.

Kamar yadda kungiyar ta ISIS ta saba, tana tsayar da bayar da tallafi ga duk wata kungiya da ke karkashinta da ta gaza kafa daula a cikin shekaru uku.

#legithausa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.