hotunan Gangamin Da kwankwaso ya hada

0 31

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Jagoran darikar siyasa ta Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Juma’a ya jagoranci wani gagarumin taron gangamin yakin neman zaben Gwamnan jihar ta Kano a karkashin jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Yusuf a karamar hukumar Bichi ta jihar ta Kano.

Taron dai wanda masu sharhi akan lamurran siyasa suka bayyana da baban gangamin an ga dubun dubatan magoya bayan tsohon gwamnan da kuma jam’iyyar ta PDP a jihar da yawan su sanye da jar hula dake nuna tsantsar mubayi’a ga jagoran nasu.

2019: Kwankwaso yayi gagarumin gangamin yakin neman zaben Kayar da Ganduje
dubun Dubatar jammaa ke nan a wajen gudanar da taron da sana kwankjwaso ya gudanar.
#kwankwasiya Facrebook

2019: Kwankwaso yayi gagarumin gangamin yakin neman zaben wancakalar da Ganduje
#kwankwasiya facebook
KARANTA WADANNAN;
1 of 104

Majiyar mu dai zata iya tuna cewa a daren Larabar da ta gabata ne dai Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya gana da wasu mukarraban tafiyar Kwankwasiyya kuma makusantan tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a wani mataki na komawar su jam’iyyar APC daga PDP. Kamar yadda muka samu, mukarraban tsohon gwamnan wadanda kuma suma ‘yan siyasa ne da Shugaba Buhari ya tattauna da su sun hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar Farfesa Hafiz Abubakar.

2019: Kwankwaso yayi gagarumin gangamin yakin neman zaben wancakalar da Ganduje
#facebook

Haka zalika cewa sauran sun hada da tsohon ma’aji na jam’iyyar APC a mataki na tarayya watau Bala Gwagwarwa da kuma tsohon shugaban hukumar nan dake kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya watau Nigerian Ports Authority (NPA) a turance, Aminu Dabo.

Cikon na hudu da na biyar din da shugaba Buhari ya tattauna da su din kamar yadda muka samu su ne Injiniya Muazu Magaji da kuma Isa Zarewa wadanda aka ce dukkan su mukarraban darikar kwankwasiyya ne.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram