[Hausa Novel]Aure ko zaman gida part 2

0 50

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

Abinda yasa naqi zuwa kuwa kiranshi maman jamila (kishiyar maman mu) tace koda ban saida tallan da ta dauramin ba kada in kuskura wani ya

KARANTA WADANNAN;
1 of 4
bani kudi yamun juye ko in bishi gida duk ranarda nayi haka sai ta yankani,Kuma zata riqa dukana
kamar yanda take dukansu jamila (yayanta kenan ).

Ashe su jamila juye suke ana ta6a lalubarsu even RR rshiyasa take chin ubansu.

naceto, Zo karakani muje tare har yace bazai jeba sai kuma yace kawo
inkaimuki na bashi ya kai ya dawo yace waranki na dari shida da talatinne ga kudin kikai wa almajirai
waran.

Yace min ko ki saida rabi kikaiwa almajirai rabi ki boye sauran kudin. Har na yarda da shawaransa sai kawai naga idan maman jamila
tagane zataci ubana tace ina nake samun kudi, Nakoma gida da wuri akace ya akayi nadawo da
wuri nayi bayani tace kar dai in kuskura in shiga motarsa kuma duk abinda ya bani kar inci, Nace to,
Tun daga ranar idan nafito talla nan zan tarar da motar mutuminnan nan kuma zan barta, Banta6a zuwa jikin motanba sai na jira audu abokin tallana yazo yakai asaye abani kudi…

Yanzu babana ya chanza yana bamu kulawa sosai kuma ya sakamu islamiya dukanmu, Inada qoqari
sosai amma su jamila sai a hankali cikin shekara daya na sauke qur’ani nashiga bangaren hadda,Namma banyi qasa a guywaba wata tara na
haddace qur’ani da tajwid da komai, Nice tafarko.

atarihin makarantarmu da ta haddace qur’ani cikin wata tara dama tun lokacinda nake karatu kamin in
iya na haddace shiyasa da nazo sai yamin sauqi nandanan na haddace, Akayi gagarumin bukin yaye dalibai hadda shugaban makarantarmu yazo nay karatu da muryar nan tawa nasamu kyaututuka sosai agurin malamanmu da manyan baqi, Yanzu na daina talla saboda baba yana iya bakin qoqarinsa.

yachanza sosai yanzu baya barinmu da tsumma kamar da mun wadata sosai, Ranar nadawo daga islamiya baba yace inzo naje gunsa sai yacemun wai aure zai nida ko nono banida za’ayimin aure gani
da qaramin jiki saboda ta dade da fara nono amma ni yar qwaila dani, Bance komaiba nace to, ko kinada
wanda kikeso nace a’ah, Aka sa ranar aurena aka dauramin aure da mijin da banta6a ganiba bansan
ko waye shiba.

Iya tunanina aurena da wani dan mashukurin mai kudi rana daya akayi shi dan jama’ar da suka taru

sunfi qarfin suzo aurena amma daga qarshe mungane gurin auren nawa sukazo,Har bayan daurin aurena ina gidanmuban tareba, Bana fita ko
ina, Sai taya maman jamila aiki, Ke in gayamaki jabo wllhy saida nayi shekara biyar agidanmu ba miji ba
labarinsa kuma ba zancen tarewa, Har na balaga, Ba miji inason inyi magana amma kunya ta hanani
yin magana duk qannena mata jamila da hafsatu an musu aure jamila da wani har ta haihu da wani ciki
ajikinta hafsatu kuma da cikinta tsoho, Nigani agida farko abin baya damuna kuma sam ban fuskantar
tsangwama agurin maman jamila, Yanzu na girma nasan miye aure saboda ina zuwa wata islamiya
dadare ta matan aure a unguwarmu.

Inajin abubuwan da ake koya mana mata da wuri suke zuwa dan suyi ta tadi, Mijina kaza mijina kaza nidai
bana ce musu komai, Abin duniya ya isheni nayanke shawarar zan yiwa baba magana sai dai kuma kunya nakeji nace ko infara yiwa maman jamila maganane inji abinda zatace.

Haka kuwa akayi, Ina biya mata karatun qur’ani bayan munqare muna hira saina cemata wai maman jamila waye mijina..?

Naji kamar bata jini ba namaimata tambayar, Ta d’ago

ido ta kalleni tace mun kitambayi babanki, Nayi shiru, Ban qara cewa komaiba, Munqare karatu da ita na
shige daki, Sai tunani kala kala nakeyi gaskiya inason sanin miye matsayina matar aure ko bazawara?

Zaman aure nake ko zaman gida?

Shekara biyar ba miji ba labarinsa sai wani niqab da baba yasani sakawa tunda aka dauramin aure, Yan
kwanakinnan nashiga damuwa sosai sai nake tunanin ko dan banida uwane aka yimin haka, Lallai
maraici hadarine, Nashiga rera kuka mara sauti nayi wata biyu Kullum sai nayi kuka duk wata walwala ta
gushe mini banida aiki sai tunani da damuwa nashiga tsaka mai wuya narame, Na kode.

Nayi baqi, Duk wata halitta ta jikina saida ta chanza..

Na yi alwashin zanyiwa babana magana, Bayan yadawo daga
kasuwa nace inada magana dashi yace to naje gurinsa, Inson inyi magana sai muryata ta fara rawa
bansan lokacinda kuka ya subucemin ba nayi kuka sosai baba ya rasa gane kaina gashi ba kowa agidan saini nima dan banje islamiya bane, Daqyar nasamu nayi shiru amma nakasa tambayarsa, Can
baba yace nasan zaki damu ace shekara biyar da watanni da daura miki aure amma bakisan mijinkiba.!

kuma baki tare Gidankiba ba ,Amma kiyi haquri nasan banmiki adalciba, Nafarko ban baki damar zabar mijin da ranki yakesoba ban tambayi
ra’ayinkiba inji shin kina sonsa ko yaya,!

Bakisan wayeba bakisan komai akansaba hasalima bakisan
wayeshiba ban barki kinyi karatun bokoba, Sannan shekara biyar dai dai da rana daya bakimin magana
ba Allah yayi miki albarka kuma mijinki wannan shekarar zai dawo insha Allah, Idan ya dawo tare
gidanki tashi kije ki kwanta Allah yayi miki albarka.

Koba komai raina yayi sanyi najin cewa mijina zai dawo wannan shekaran dan wllhy na gaji da zama
da igiyar aure akain.

mu hadu a kashi na uku

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram