[Hausa Novel] Ruwan Kashe Gobara Kashi Na 5 zuwa na 10

0 123

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

CIGABAN RUWAN KASHE GOBARA

_6_

~~~ Tsaye barrister elmustapha yayi yana tunanin lallai zamanin yanzu abun tsorone domin mutane sam basuda tausayi kadanne daga ciki masu jin tsoron Allah,

Agogon dake daure a hannunshi ya kalla misalin karfe 1 nadare gashi sai ruwan sama ake tsugawa kamar da bakin kwarya,

Yadade atsaye kafin dr din yafito yazo ya sanar dashi cewar patient dinshi ta farfado zai iya shiga ya ganta,

Cikin halin tausayawa ya shiga dakin da take, tana kwance da drip ahannunta ana kara mata,

Jiyowa tayi ahankali tana kallonsa kallo irin na kurulla, bakine dogo mai dan jiki amma ba can ba,

“Sannu baiwar Allah, yajikin naki?” Yace da ita daidai lokacin da ya karasa bakin gadon da take,

Idanuwanta masu mutukar girma ta dago tana kallonsa cikeda tambayoyi fal abakinta,

“Bawan Allah inane nan? Wanne garine wannan? Meya kawo ni nan? Meya sameni?”

Kallonta yayi da dan murmushi akan fuskarshi,

“Kiyi hakuri baiwar Allah, wadannan tambayoyin naki duk zan sanar dake amsoshinsu amma sai bayan komai ya daidaita”

Kanta ta girgiza hawaye na bin kuncinta sakamakon tunowa da tayi da ko ita wacece, motsi ta danyi da zummar gyara kwanciyarta amma sai ta kasa sanadiyyar wani irin radadi da ya ratsa kasanta,

Kallonshi tayi akaro na biyu “dan Allah ka sanar dani abinda ya sameni, wallahi ban san abinda yafaru dani ba, jikina ciwo yake, ina jin wani irin zazzafan ciwo atare dani,ga wani zazzabi mai zafi da nake ji”

Tausayine ya kamashi to amma baya son sanar da ita halin da ta tsinci kanta aciki yanzu saboda yasan dolene hakan yayi mata ciwo duk da cewa bashida tabbacin cewar ita budurwa ce ko sabanin haka,

“Kiyi hakuri kar ki daga hankalinki, insha Allahu zaki samu lafiya nan bada jimawa ba,kuma zan baki dukkan amsoshin wadannan tambayoyin naki”

Idonta ta mayar ta rufe tanata sake saken abubuwa acikin ranta, ita dai iya tsawon rayuwarta bata taba sanin wani gari makamancin wannan ba sai gashi yau ta tsinci kanta aciki ko inane Allahu a’alamu,

“Nasan kina bukatar abinci bari naje nagani ko zan samo miki”

Kai ta girgiza masa “kar kayi wahalar nemo min abinci domin banida bukatarsa ahalin yanzu”

“To shikenan ni zanje natafi gobe da safe insha Allahu zan dawo”

“Allah ya kaimu”

Tabashi amsa tana bin bayanshi da kallo, ita dai ba saninshi tayi ba asalima bata taba ganinshi ba sai yau, tunani taci gaba dayi har bacci ya samu damar dauketa.

Washe gari kamar yadda ya alkawarta misalin karfe 8:30 yadawo asibitin anan ya samu likitan ya karbi sallama bayan an harhada masa magungunan da zata rinka sha sannan likita ya jaddada masa cewar suna komawa gida ta shiga ruwan zafi.

Dakin da take ciki ya shiga, azaune akan gado ya isketa tayi tagumi, jin alamun shigowar mutum ya sanyata dagowa tana kallonsa, shima ita yake kallo komai na jikinta dankare yake da dattin dauda, yanda ya kawota jiya da daddare yau dinma haka take dauke da kayan da tayi rayuwar tabin hankali dasu,

“Sannu ko, taso muje gida likita ya sallameki” yace da ita,

Mikewa tayi ahankali ta sauko daga kan gadon tafara takawa ahankali saboda har yanzu bata ji saukin jikinta ba, bin bayanshi tayi har harabar asibitin inda ya adana motarsa awurin da aka tanada musamman domin adana abin hawa.

_7_

~~~Bud’e mata kofar motar yayi ta shiga ta zauna, ita dai binsa take kawai da kallo hakama dukkan wuraren binsu take da kallo ba tare da tace uffan ba,

Motar yayiwa key suka fita daga harabar asibitin, cikin gari suka hara yana tuki sannu ahankali cikin nutsuwa da kwarewa har suka isa wata unguwa mai karancin gine gine,

Agaban wani dan madaidaicin gida ya yayi packing yafita ya bude gate ya shigar dasu cikin gidan, fitowa tayi daga cikin motar kamar yadda shima ya fito, bin bayanshi tayi suka tasamma cikin gidan Wanda daga gani babu tambaya gidan mace daya ne,

Matar gidan tana hakince acikin falo suka sameta tadora daya akan daya, ganinsu ya sanyata mikewa tsaye tana kare musu kallo,

“Barrister wacece wannan?” Ta tambayeshi tana huci,

“Ki kwantar da hankalinki ni’ima zaki san ko wacece nan bada jimawa ba amma yanzu abinda nake so dake kinga ayanayin da take to ina so ki kaita tayi wanka ta shiga ruwan zafi sosai kibata kaya ta shirya ta saka kafin tazo taci abinci”

Kamar zata sake magana sai kuma ta fasa ta juya tayi gaba,

“Bi bayanta” yace mata yana nuna mata hanya,

Binta tayi sumi sumi duk kanta adaddaure, amma daga gani tasan za asamu matsala,

Wani daki taga matar ta shiga dan haka itama tabita ciki,

“Ga towel, ki shiga bathroom akwai dukkan abun bukata aciki sannan idan akwai wani abu wanda kike bukata sai kiyi min magana”

Karbar towel din tayi ta shiga bathroom din batare da tayi magana ba, fuuuu! Ni’ima tayi falo inda elmustapha yake zaune tana zuwa ta tsaya agabanshi cikin masifa tafara magana,

“Wai wacce yarinyace waccen ka kawo min ita gidannan sannan tsabar rainin hankali har kana sanar dani cewar wai ta shiga cikin ruwan zafi sosai, meye alakarka da ita?”

“Haba ni’ima ki kara hakuri mana ai zan sanar dake komai”

“Kaga malam babu wani hakuri kawai ka sanar dani inda ka samota”

“Ni’ima wallahi ban santa ba mahaukaciya ce kuma muna kyautata tsammanin ta samu lafiya yanzu shiyasa nayi niyyar taimakon ta”

“Yanzu naji batu” tafada tana murmushi,

“Bari naje na fiddo mata da kayan da zata saka,juyawa tayi tafita daga falon tabar elmustapha tsaye yana kallonta yana murmushi saboda sanin zafin kishi irin na ni’ima.

Tsayawa tayi agaban mudubin dake manne a bangon bathroom din tana kallon jikinta da fuskarta, hawaye ne suka fara bin fuskarta, dakyar ta iya samu ta tsaida hawayen ta tari ruwan zafi ta zauna aciki,gashin kanta mai mutukar tsawo da yawa tafara wankewa wanda sai da yaci ruwa bokiti 3 kafin dattin dake jiki ya fita,

Wanka tayi ta sake karawa sannan ta dauraye jikinta tafito bayan ta yi alwala,

Jinta take kamar sabuwar halitta gashi iska sai shigarta take yi tako ina, acikin dakin ta iske ni’ima tana tsaye tana zabo mata sutturar da zata sanya ajikinta,

“Har kin fito?” Ni’ima ta tambayeta cikeda fara’a, kai kawai ta daga mata batayi magana ba,

“Kiyi hakuri kinji,ki sanar min da sunanki saboda ban san da wanne suna zan kiraki ba” ni’ima tasake yi mata wata maganar tana kokarin rufe akwati,

“Sunana IKHLAS”

Yanda tayi maganar asanyaye ahankali cikin sanyin murya ya sanya ni’ima jin tausayinta,

“Allah sarki ikhlas, to ki shirya ga kaya nan ki saka sai kifito muci abinci kinji”

“Nagode” ikhlas ta bata amsa tareda dosar wurin da ta ajiye mata kayan,juyawa ni’ima tayi tafita daga cikin dakin tabar ikhlas domin ta shirya.

_8_

~~~ Ba wata doguwar kwalliya tayi ba, mai kawai ta shafa sai farar powder da ta gogawa fuskarta amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba,

Kayan da ni’ima ta ajiye mata ta dauka ta saka, riga da skirt ne na bakin leshi mai tsananin tsada da kyau, dinkin yayi mata kyau ajikinta domin ya bayyanar da shape dinta afili,

Sallah tayi raka’a biyu kafin ta fita zuwa falon gidan, ni’ima da elmustapha ta gani zaune suna zaman jiran fitowarta domin yin breakfast,

Ido elmustapha ya zuba mata yana kallonta domin ba karamin kyau tayi masa ba, babu wanda zai ganta yayi tsammanin ta taba samun tabin hankali, gata takai duk inda wata kyakkyawar mace takai, tausayinta yaji yana shigarsa saboda tunowa da yayi cewar yanzu ita ba budurwa bace sakamakon fyaden da wani marar tausayin yayi mata amma shi yana da yakinin cewa har yanzu ita bata da masaniyar abinda ya faru da ita,

“Ikhlas kin fito? Karaso nan muci abincin”

Muryar ni’ima ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula,

Anutse cikin nutsuwa ikhlas ta karasa ta zauna akusa da ni’ima amma har lokacin shi elmustapha bai bar binta da kallo ba,

Soyayyen dankali da kwai ni’ima ta shirya musu sai ko tea, zubawa ikhlas tayi ta mika mata sannan ta zubawa elmustapha nasa ta ajiye masa agabansa,

Babu wanda yayi magana sai dan lokaci zuwa lokaci da elmustapha yake dan yiwa ni’ima hira, da haka suka kammala cin abincin.

KARANTA WADANNAN;
1 of 4

Gyaran murya elmustapha yayi ya juya yana kallon ikhlas sannan ahankali yafara magana,

“Baiwar Allah hakika ki godewa Allah da ya baki lafiya adai dai lokacin da baki sani ba kuma baki tsammata ba, kisani rayuwar da kika yi abaya lokacin da kike hali na rashin lafiya to Allah ya dauke alkaluma akanki amma ahalin yanzu andawo da alkaluman rubutu akanki za arinka rubuta dukkanin ayyukanki na alkairi ko sabanin haka, Allah yasa kaffarace sanadiyyar rashin lafiyarki, sannan idan kin kwana biyu kin nutsu kin huta zan kaiki har gaban iyayenki, yanzu nan kina cikin garin yola ne babban birnin jihar Adamawa amma ina son ki sanar dani ainihin labarinki kafin ki hadu da lalura”

Ko dagowa ikhlas ba tayi ba amma kuma da alama kuka take yi marar sauti Wanda iya hawaye ne kawai yake kwarara daga idanuwanta.

Zazzabine mai mutukar zafi ya sake rufe Lamido nan ya shiga surutai marassa kan gado dama shi yana dadewa baiyi rashin lafiya ba amma duk lokacin da kuma ta kamashi to yana jigatuwa,

Kudundune yake shi kadai adakin nasa sai maganganu yake,

“Washh zazzabin nan Allah yasa iya ni kadai ne bai kama min ke ba, washh jin kaina nake kamar zai tsage, bash dan Allah kaje ka samo min ita..!, washh innah, innah, innah, Baffa wayyo baffah, inna, innah, innah..!”

Haka yayita fada har bacci ya samu nasarar daukeshi sai alokacin bakinsa yayi shiru, ya dan jima yana bacci kafin ya iya farkawa.

_9_

~~~Jikinsa amace ya tashi har lokacin da sauran zazzabin ajikinsa,hawaye ya fara yi yatashi ya nufi part din innah,

Yana shiga ya sameta zaune a falonta tana kallon tv,tana ganinshi ta mike taje ta rungume shi,

“Lamido jikinne? Dadina dakai rangwanta daga rashin lafiya ta kamaka sai ka zauna kayita kuka, kai dai akomai jarumi ne amma banda a bangaren jinya domin komai kankantar rashin lafiya kuka kake yi mata”

Kan doguwar kujera ta kaishi ta kwantar dashi tafara shafa sumar kanshi tana murmushi,

“Baka ci abinci ba, in kawo maka ko?”

Kai ya girgiza alamun a’a,

“Haba Lamido ka daure kaci mana sai kasha magani, kaji lamidon innah”

Juyawa yayi ya gyara kwanciyarsa, hakan ya sanya inna tashi ta shiga kitchen taje ta bararrako masa indomie ta kawo masa, har lokacin yana kwance yana kuka,

“Tashi kaci sarkin kuka”

Tayar dashi zaune inna tayi tafara bashi abaki yana ci har ya dan ci dayawa, panadol ta dauko masa tazo tabashi yasha,

Kwanciya ya sake yi har lokacin salla yayi sannan ya mike yashiga bedroom din inna ya je ya dauro alwala yafita zuwa masallaci,fitowa yayi bayan an idar da salla anan ya hadu da bash yana kokarin shiga gidan,

Packing bash yayi ya fito yana murmushi,

“On top” bash yafada gamida mika masa hannu, mika masa hannun shima Lamido yayi yana dan murmushi,

“Bash ya akayi”

“Normal, ya jikin naka? Kazo mu shiga sch mana”

“Kayi salla ne?”

Lamido ya tambayeshi,

“Muje kawai sai la’asar tayi sai nahada nayi”

Kallonshi Lamido yayi “bash baka tsoron Allah, kayi duk iskancin da zakayi agarin nan amma ya zamana tsakaninka da ubangijinka akwai alaka mai kyau,ni ka ganni nan duk iskancin da kaga ina yi to ina yin salla akan lokacinta sannan bana taba bari da ta wuceni sai dai idan acikin hali na lalura”

“Naji muje ka shirya mu fita”

Wucewa suka yi suka nufi cikin gidan Lamido sai faman yayyamutsa fuska yake yi irinta marassa lafiya,

Wanka Lamido yayi ya fito ya shirya cikin jar t shirt da bakin trouser, rigar ba karamin kamashi tayi ba,

Fita suka yi suka nufi cikin gari bash yana driving Lamido yana zaune agefenshi yana kallon gari ta cikin glass,

“Lamido ya jikinne? Wai kodai…?” Bash ya fada cikeda tsokana,

Yamutsa fuska Lamido yayi sannan ya danyi wani basaraken murmushi, “bash ban taba yin zazzabi irin na jiya ba, kai ni rabon ma da nayi zazzabi har namanta sai wanda nayi jiya”

“Shiyasa nace kodai…?”

“Bash mubi ta wannan hanyar ko Allah zai sa muga wannan yarinyar”

“Angama ranka ya dade, on top”

Murmushi Lamido yayi yaci gaba da rarraba manyan sexy eyes dinshi yana bin ko ina da kallo domin yanzu bashida burin da ya wuce na ya sake haduwa da wannan mahaukaciyar yarinyar.

_10_

~~~Har suka bar harabar wurin da ya hadu da mahaukaciyar nan jiya bai ga koda mai kama da ita ba hakan ba karamin tayarwa da Lamido hankali yayi ba,

Cikin makarantar su suka shiga,suna shiga yan mata suka fara washe baki suna bin motar da kallo,

“Lamido na mata, mata suna sonka” bash yace dashi,

“Nima ai ina sonsu” Lamido ya bashi amsa yayinda yake zaro wayarshi daga cikin aljihun jeans din dake jikinsa,

“Bash dan Allah ka taimaka min mu nemo yarinyar nan tajiya, wallahi bash ina ji ajikina i can’t do without her..”

Cikin sauri bash ya kalleshi,

“On top anya kuwa yarinyar nan ba aljana bace? Kai ina jin kila aljana ce tazo maka a siffar mutane har ka kusanceta shiyasa ka kasa mantawa da ita idan ba haka ba yan mata nawa kayiwa dabara ka rabasu da budurcinsu amma duk hakan bai dameka ba sai wannan wacce ko hankalima bata dashi, tababbiya”

Sai da Lamido ya Ciro kodin daga aljihunsa yafara sha sannan ya kalli bash ya lumshe idanuwansa masu mutukar girma,

“Bash ina son yarinyar nan wallahi..”

“That’s why nace aljana ce duk yadda aka yi, Lamido kaifa baka taba son wata mace ba sai dai ita ta soka, amma yau kana furta cewa kana son wata mace with your mouth, macen ma mahaukaciya marar hankali, kai gaskiya da walakin wai goro a miya”

Bude idonshi Lamido yayi ya danyi dan karamin tsaki,hannu yakai ya taba wuyanshi,

“Kaga ni ka kyaleni pls, zazzabi nake ji”

“Zazzabi kuma? Allah Lamido ina jin gamo kayi”

Murmushi Lamido yayi yakai dubanshi zuwa ga window din motar, ta glass yafara hango daliban makarantar sunata kai komo kowa yana sabgar gabanshi,

Glass din saitin da yake aka kwankwasa,a kasalance ya sauke glass din yana kallonta,fadila ce budurwarsa tana sanye cikin leshi kalar ruwan madara tasha kyau har ta gaji,

“On top ya akayi” tafada tana rankwafowa kusa da fuskarshi,kallonta yayi ya dauke kanshi batare da yayi mata magana ba, kallonshi itama take acikin ranta kuma tana cewa

“Kaji matsalarshi ai wannan gayen mugun dan rainin hankali ne,yanga kamar wani mace ga shegen jan ajin tsiya”

Amma afili sai ta dan yi murmushi takai hannunta ta kamo nashi,

“On top ya naji jikinka da zafi, ko baka da lafiyane”

Sai da ya dan lashi lebenshi nakasa har dimple dinshi yafito sannan yace,

“Bana dan jin dadine yau”

“Ayya sorry, Allah yabaka lafiya”

“Thanks” yafada yana kokarin daga glass din, sanin halinshi ya sanya fadila matsawa ta juya ta tafi, tana tafiya ya ji bash yana yi masa magana,

“On top kana yarfa yarinyar nan fa gaskiya, wlhi ka sauya hali”

“Bash muje gida ka saukeni zazzabi nakeji”

Yafada yana kankame jikinsa sakamakon sanyin da yafara ji yana bugarsa.

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram