[Hausa Novel] Aure ko zaman gida 1

0 61

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram

AURE KO ZAMAN GIDA 1 by
KARANTA WADANNAN;
1 of 4
HAUWA M.JABO

akan hanyar asibiti nida qawata zeenah khalifa zamuje duba wata maqociyarmu da batada lafiya,Muna shiga asibiti mukayi karo da wata mata da yara guda biyu a hannunta zenah khalifa tayi sokoko tana kallonta.

Ke zeenah khalifa kinji haushi
ki kalli maza ki kalli mata.! Banason wulaqanci hauwa jabo.!

Mikike nufi da inkalli mata in kalli
maza? kamar wata bunsura..!!!

Na kwashe dadariya nace yanzu dai yimin bayani mi kika hango.??

Ta kwashe da dariya kibari kawai,Hauwa jabo matar nan ta hadu billahillazi.

Da ace ba baqa bace sai ince
wllhy ba indiyace keni muje muyi qawance da ita,Ke zainab muna fama da talaucinmu zamuje gurin masu kudi.?

Bazanje a wulaqantaniba gaskiya,Ke
Hauwa jabo wllhy kin cika tsoro,Idan bazakiba bari inje ingabatarda kaina,Ta kwace wayata taje tana
kuri.

Bansan yanda sukayiba naga har sunyi musanyar number suna yiwa juna murmushi wani namiji yazo naga yana mata magana tay murmushi ya rungumeta hannunsa dayan hannunsa riqe da handbag dinta ya mata kiss a kumatu ina tsaye ina kallo araina nace dama matan nigeria suna soyayyah haka?

In shot sun burgeni kuma inason
inji tarihinsu da inda suka iya soyayyah irinta Iranian saboda Iranian ne kawai zakiga sundaukarwa
matansu jaka su rungume jariri kuma su rungume matar kamar wani zai kwace musu.. !

Zainb ta dawo sai murna takeyi ina tsaye,Sai wangale baki takeyi
zainab,Amma fa matar ta haduko H jabo?

uhumm ba laifi!, Ke Wllhy kincika matsala,! Nidai muje, Zamu
shiga kenan sai gasu sun fito suna dagawa zainab hannu sai wangale baki take har yar wushiryarta da
dan dimple dinda take kuri dashi ya fito araina nace zainb ansamu aikin yi, Munshiga mun duba mara lafiya munfito muka wuce city plaza muka dan sayi ice cream muka samu keke nupin sai gida.

Eshqi mano too..

tuye qalbam mimune

“zandagi batu behtare”

Ringtone din zainb kenan kuma
gashi tashiga wanka naga anrubuta sister zainb araina nace waye kuma sister zainb..

hello, hello

namesake, nasissim adaya banqaren naji dafada cike da dariya.

Araina nace wannan yar turkiyace
ni jabo ba Turkish na iyaba hakadai na amsa mata nasissim eyem ebit ta kwashe da dariya.

Araina nace zatace ban iyaba na kwabsa, Sai tace ni ban iya wannan da kika fadaba nima nay dariya, Tace
yaushe zaku zo gidana da sauri nace gobe zamuzo ba matsala, Eh kuzo ta fada cike da shauqi, Ta bani address dinta na rubuta zeenah khalifa na fitowa nace namesake dinki takira tace gobe muzo.

ihuuuuuuhw.!! Wani ihu tayi tanajin dadi nima naji dadi ko banxa inason muje inyo gulma…

Tun safe kinsan yau zamuje unguwa ko?

Unguwa kuma.?

Lallai wllhy jabo kinji dadinki kin manta zamuje gidan namesake dina.!!??

Au natuna qarfe nawa ma zamuje.?? 12 mukace mata. Kk.. mun isa gidanta wani qaton gidane da shuke shuke ya rufe ko ina nace anya nanne zainb karmuje a cire mana kai, Eh nanne mana muka danna bell maigadi yabude mana yace su zainb ko mukace eh kushigo, Araina
nace har angayawa maigadi zamuzo Lallai anaji damu..

Munsameta tsakiyar gida tana ganinmu tazo ta rungume mu….

muje zuwa muji yanda hauwa jabo
zatayo mana gulma agurin zainab.
Munci munsha mun hole anan na fahinci zainab tanada balaeen saurin sabo kuma akwai tsiwa da wasan rainin hankali, Nandanan muka saba da ita amma naga tafi maida hankali gurina ko dan taga nafi hankaline ohoo..?

Watannmu uku da sanin zainab duk ansanmu a gidanta tana zuwa gidanmu sosai,Ranar munje
gidanta, Nan nanemi ta bamu labarinta daga farko tayi gardama daga baya mitayi tunani ta amince
naso inyi shishigi intambayeta amma sunyi rayuwa a iran ko amma sai nafasa nace bari in barta kawai
maji daga baya…

Tun safee nazo inji gulma nikadai nazo saboda nasan idan nazo da zeenah khalifa to labarin bazaimun dadiba, Nayi sa’a tagama aikinta gaskiya zainab tanada kazar kazar batada son jiki ko kadan, Takawomin fresh milk nashanye, Ta gyara zama ta
fara bani labari kamar haka………

Sunana zainab Abdullahi mahaifiyata gurin hai huwata Allah yamata cikawa, Mahaifina mutum ne
mara kulawa sosai, Sam bai damu da tarbiyarmu ba baidamu da chin muba bai damu da shanmuba, Gamu mu mu shida ne a gidan ni kadai nake agun
mamata data rasu sauran biyar din duk yayan kishiyar mamanmune maza uku mata biyu,Agurin
kishiyar mamata na girma, kishiyar mamata mutumce wacce batayi dan Allah idan kikayi mata zata miki idan baki mataba to bazatayi mikiba,Amma bata cutar da kai sai ka cutar da ita, Tana dauramin
tallan kayan miya ranar da nasiyar to zamuji dadi idan kuwa yayi kwantai to bamu ba abinci sam saboda da dan ribar da take samune take bamu
abincin safe dana rana, Nadare kuwa baba yake bayarwa.

Bata ta6a dukanaba kuma bata cika yimin fadaba amma tanacin uban yayanta sosai nice babba agidan, Banta6a sanin hanyar makarantar
bokoba balle ta addini har nakai shekara goma sha daya bana karatu sai yawon talla, Ina sha’awar boko

wasa wasa har nafi amina iya karatu sai tafara jin haushi saboda musun da nake mata akan wannan haka yake tace a’a ba haka yakeba, Haka yake
tadaina koyamin komai ataqaice duk wata takardar qosai ta unguwarmu idan nagani sai nakaranta na iya hada kalmomin english inkaranta amma bansan ma’anarsuba ke intaqaita miki jabo duk wani karatun indai karantawane ina iyayi da rubutawa…..
Akwai wata rana na fito tallan wara saboda yanzu nadaina tallan kayan miya wara nake talla yafi kasuwa ina tafiya naga wata qatuwar mota baqa
baka ganin waye aciki,Anyi parking dinta a gefen hanya, Kusan wata daya Kullum sainaga motarnan wani yaro yace wai mai motan yace ki kawo wara na kalli motan lokacin iya tunanina nasan mai Wannan qatuwar mota bazai ci waraba, Nace bazanje,

Shegiya matsiyaciya arziki yana kiranki kina gudu kar kije miya dameni wannan mutumin duka yake siya yace kikai masallaci………

Mu hadu a kashi na biyu

Taba nan ka dauko Affilikashon din mu na dauko hoto da Bidiyo a Instagram