Har da farar fata a cikin yan Boko Haram

0 5

Click to subscribe my channel

Rundunar sojin Najeriya, ta ce har da farar fata a
cikin ‘yan Boko Haram din da ta kama, yayin
fatattakar ‘yan kungiyar daga dajin Sambisa.
A ranar Asabar ne dai shugaban Najeriyar,
Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan kasar albishir
cewa an karya lagon Boko Haram.
Kakakin hedikwatar tsaron Najeriyar, Birgediya-
Janar Rabe Abubakar, ya shaida wa BBC cewa sun
kama ‘yan Boko Haram da dama da suka hada da
bature a dajin na Sambisa.
Sai dai kuma Rabe Abubakar mai fayyace ko
baturen dan wacce kasa ne ba.
Ya kuma ce an yi dauki ba dadi kafin a karbi dajin
na Sambisa.
“Mun kama su, mun kakkashe wasu sannan mun
shiga wurin da suke ajiye makamansu.” In ji Rabe.
Kakakin Hedikwatar tsaron ta Najeriya, ya kara da
cewa ” yanzu haka sojojinmu ne kawai a dajin
Sambisa, babu dan Boko Haram, idan kuma akwai
su to sun buya kuma za mu kai gare su.”
To amma dangane da batun ko ina Abubakar
Shekau ya ke, Rabe ya ce “muna yi ne domin
karya Boko Haram ba wai don mutum daya ba.
Shekau daya ne daga cikin ‘yan kungiyar. Abu
mafi a’ala shi ne mun karya Boko Haram.”
Sharhi, Usman Minjibir, BBC Hausa
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da Najeriya
ke ikrarin fatattakar Boko Haram amma kuma daga
baya sai labari ya sha banban.
Sau fiye da biyu rundunar sojin Najeriya ke cewa
ta kashe ko kuma raunata shugaban kungiyar,
Abubakar Shekau, amma ‘yan kwanaki bayan nan
sai Shekau din ya yi raddi.
Har wa yau, wasu na ganin ta ya ya za a gama da
Boko Haram amma kuma ba a iya ceto ragowar
‘yan matan Chibok din ba fiye da 200.
Sai dai kuma masana harkar tsaro na cewa
watakila akwai kanshin gaskiya dangane da ikrarin
da kasar ta yi cewa ta karya wa Boko Haram din
lago, a wannan karon.
Masanan sun dogara ne da irin banbancin hare-
haren ‘ya’yan kungiyar na yanzu idan aka kwatanta
su da na baya musamman a 2014 da kuma farkon
2015.
A baya dai ‘yan Boko Haram na iya shiga duk inda
suke so, su kuma aiwatar da irin hare-haren da
suke son kaiwa.
Amma yanzu za a iya cewa al’amarin ya koma
yakin sunkuru ta hanyar kai hare-haren kunar
bakin-wake.
Sai dai kuma masharhata kan tsaron sun nemi
dakarun Najeriyar da su sake sabon salon yaki
domin idan kida ya sauya to ya kamata rawa ma ta
sauya.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Click to subscribe my channel