Gwamnatin Tarayya ta rage Kudin JAMB,NECO,BECE

0

Gwamnatin tarayya ta bayar da izinin rage farashin kudaden daukar jarabawa shiga jami’a na JAMB da kuma jarabawa kammala karatun sakandire na NECO da kuma jarabawar BECE.

An samum amicewar ne a taron majalisar zartarwa na gwamnatin tarayya FEC wadda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa na Aso Billa Abuja.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya yi wa manema labarai jawabi a kan sakamako zaman majalisar, ya kuma kara da cewa, daga watan Janairu na shekara mai zuwa, masu neman dana jarabawar shiga jami’a na JAMB za su rinka biyan Naira 3,500 a maimakom Naira 5,000.

Ga dalibai masu kamala karatun sakare kuma ‘Senior Secondary Certificate Edamination (SSCE)’ za su biya kudin jarabawar NECO a Naira 9,850 maimakon Naira 11,350 da ake biya a yanzu.

Haka kuma Ministan ya ce, an rage kudin BECE daga Naira 4,000 zuwa Naira 5,500.

KARANTA WADANNAN;
1 of 93

#leadershipayau