Gwamnatin Kano Ta Tsige Babban Akawunta A Bisa Zargin Yiwa Kwankwaso Leken Asiri

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin jahar Kano a karkashin shugabancin
Abdullahi Ganduje ta sallami babban akawun
jahar Danjuma Adamu daga aikinsa a sakamakon
zargin da ta ke yi masa na yin leken asiri akan
bayanan kudaden da gwamnati ke samu da kuma
mika wannan bayanai ga tsohon gwamna Rabiu
Musa Kwankwaso, wanda a yanzu haka sanata
ne mai wakilatar Kano ta tsakiya.
Gwamnatin ta kuma zarge shi da yi mata zagon
kasa na toshe kafofin da gwamnatin ke karbar
kudade, al’amarin da ya haddasa jinkiri wajen
biyan albashi ga ma’aikatan jahar.
A wata sanarwar da aka turawa manema labarai
a ranar Lahadin da ta gabata mai dauke da sa
hannun kwamishinan yada labarai na jahar,
Mallam Muhammad Garba, an bayyana cewa
Mallam Adamu zai mika mukaminsa ga direktan
ma’adanai na ma’aikatar kudin jahar, Ibrahim
A.M. Kura, wanda shi ke kan layi a girman
mukami.
Ganduje ya yiwa babban akawun mai barin gado
godiya a bisa aikin da ya yiwa jahar kuma ya yi
masa fatan alkhairi a ayyukan da zai yi nan
gaba.
A watan Mayun bana ne dama majalisar jahar
Kano ta baiwa gwamnan shawarar ya tsige
babban akawun.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Get real time updates directly on you device, subscribe now.