Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Soke Ayyukan Hukumar Hisba A Jihar

0 2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Gwamnatin jihar Sokoto ta haramta hukumar Hisba a duk fadin jihar kamar yadda Kwamishinan lamuran addini na jihar Alhaji Mani Katami ya bayyana.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe hukumar Hisba din ne sakamakon rikicin da ya dabaibaye hukumar.

KARANTA WADANNAN;
1 of 236

Kwamishinan ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai sanarwar kashe hukumar a jiya Lahadi bayan zaman da suka yi a ranar Asabar kan batun shawo kan matsalar
hukumar.

In ba a manta ba hukumar Hisban ta kai samame a wurin kamun kunshin diyar gwamnan jihar Aminu Tambuwal inda ta kama kayayyankin kidan da aka yi amfani da su wajen shagulgulan bikin inda DJ din ya bar kayan kian ya ranta a na kare.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.